Manjo Hamzah Al-Mustapha ya fadi yadda ‘kudin Abacha’ su ka bar Najeriya
Hamza Al-Mustapha, wanda ya rike mukamin shugaban masu kula da Sani Abacha a lokacin ya na mulki, ya yi magana game da kudin da ake zargin gwamnatinsa da sacewa.
Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi wa Jaridar Vanguard bayani a kan yadda aka rika tattara kudin Najeriya ana fita da su a lokacin mulkin na tsohon shugaban kasa Sani Abacha.
Al-Mustapha ya ke cewa ya fara jin labarin ‘satar’ gwamnatin Abacha ne a lokacin da ya ke daure a gidan yarin Kirikiri. An rufe Al-Mustapha a gidan yari na shekara da shekaru.
Tsohon CSO din ya ke cewa ba a taba tuntubarsa ba game da wannan kudi, kuma bai da wata alaka da zargin, asali ma Manjon ya ce wannan badakala abin kunya ne a kansa
A cewarsa, hankalinsa bai kwanta ba a lokacin da ya fara jin labarin badakalar, domin kuwa ya san yadda Marigayi Janar Sani Abacha ya ke da adana da rashin facakar kudi.
Ya ce: “Abin da na sani shi ne akwai lokacin da Amurka, Ingila da wasu Kasashe biyu su ka sa wa Kasar Najeriya takunkumi saboda wasu sun dauko fada da Janar Sani Abacha.”
KU KARANTA: PDP ta ce ana neman mikawa wani Gwamna kason kudin satar Abacha
Dogarin tsohon shugaban kasa Abacha ya bayyana cewa wasu manyan ‘Yan Najeriya ne su ke fada da gwamnatin Sojin Abacha a wancan lokaci, har aka sa wa kasar takunkumi.
“Domin maganin wannan takunkumi, tsohon shugaban kasar ya bukaci ya yi magana da Masu ruwa da tsaki daga Arewa da Kudancin Najeriya game da wannan mataki.” Inji sa.
“An yi wannan taro ne domin duba hadarin takunkumin da aka sanyawa Najeriya a wajen fadar shugaban kasa, domin dakin taron Aso Villa ba zai dauki adadin jama’an ba.”
Al-Mustapha ya kara da cewa: “Matsayar da aka cin ma shi ne Najeriya ta fitar da kudi ta hannun mutanen da ke kasuwanci a waje, ta haka kasar za ta iya shigo da fitar da kaya.”
Fitaccen Sojan ya ce a dalilin haka ne kudin Najeriya su ka fada hannun mutane a kasar waje, wanda yanzu ake dawowa Najeriya da kudin da sunan satar da gwamnatinsu ta yi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng