Naira Marley ya yi magana bayan Budurwa ta fito da bidiyonsa a dakin Dubai

Naira Marley ya yi magana bayan Budurwa ta fito da bidiyonsa a dakin Dubai

Wata Baiwar Allah mai matsakaicin shekaru ta fito da wani bidiyo inda aka ga fitaccen Mawakin nan Naira Marley a kan gado ya na barci.

Wannan Budurwa ta yi ikirarin cewa ta dauki bidiyon ne bayan sun gama holewarsu tare da Mawakin a wani otel a kasar Larabawa.

Idan bidiyon ya tabbata na gaske, an yi wannan danyen aiki ne a Birnin Dubai da ke kasar UAE a Yankin Gabashin Nahiyar Asiya a Duniya.

Wannan Mata da sunan ta bai bayyana mana ba tukun, ta bayyana cewa sun kwana da Mawakin ne a katafaren otel dinnan na Burj Al Arab.

Burj Al Arab ya yi suna a Duniya inda jama’a su ka saba zuwa domin su huta. Kudin kwanan daki a otel ya kai N500, 000 a kudin Najeriya.

KU KARANTA: Jami'an FRSC sun fasa tayar motar da ta dauko Wata Mai juna biyu

An wallafa wannan bidiyo a shafin Instablog na Instagram. Fiye da mutane 500, 000 su ka kalli wannan faifai a wannan dandalin na zumunta.

A bidiyon an ga wannan Budurwa ta nuna fuskarta cikin farin ciki. Ba dai wannan ba ne karon farko da Naira Marley ya jawo abin magana.

Asalin sunan Mawakin Azeez Fashola, kuma shi ne shugaban gungun wasu Matasan zamani da su ke kiran kansu Marlians yanzu a Najeriya.

Bayan wannan bidiyo ya fito, Matashin Mawakin ya fito gaban Duniya ya bayyana cewa bai ji kunyar komai ba, domin dama can bai da kunya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel