An kama wanda ake zargi da kashe Fasto yayin da ake bikin aurensa a Imo

An kama wanda ake zargi da kashe Fasto yayin da ake bikin aurensa a Imo

Wani Mutumi da ake tunanin cewa gawurtaccen Mai garkuwa da mutane ne ya shiga hannun Dakarun ‘Yan Sandan SARS, inda aka yi ram da shi a jihar Imo.

Kamar yadda mu ka samu labari dazu, ana zargin wannan Bawan Allah da hannu wajen garkuwa da kisar Limamin kiristan nan, Rabaren Cyriacus Onunkwo.

‘Yan Sanda sun bada sunansa a matsayin Charles Nnanna. Nnannan ya ruga can kasar Indonisiya ne bayan sun hallaka wannan Fasto a shekarar 2017.

Jami’an tsaro na SARS sun kama wannan Mutumi ne a Garin Aji da ke cikin karamar hukumar Oru ta Gabas, a jihar Imo a cikin tsakiyar Watan Fabrairun jiya.

An yi ram da Mista Charles Nnanna ne a lokacin da ake daura masa auren gargajiya da Mai dakinsa. Jaridar nan ta The Nation ta fitar da wannan rahoto.

KU KARANTA: Gini ya fadowa wani 'Dan kwadago a jihar Legas har ya mutu

Rahotannin sun bayyana cewa Nnanna ya na cikin gungun masu garkuwa da mutanen da su ka sace Rabaren Onunkwo, a karshe su ka aika sa zuwa barzahu.

Kakakin Jami’an ‘Yan Sandan jihar Imo, SP Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da cewa Charles Nnanna ya na hannunsu, har kuma ya amsa laifinsa da kansa.

Orlando Ikeokwu ya shaidawa ‘Yan jarida a madadin ‘Yan Sandan jihar Imo cewa za a gurfanar da Nnanna a gaban Alkali domin a yanke masa hukuncin da ya dace.

‘Yan Sanda sun yi nasarar kama sauran Abokan aikin wannan sabon Ango tun kwanakin baya. An gaza damke shi ne bayan shi ya sulale ya bar kasar a lokacin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel