Bola Tinubu ya yabawa kishi, amana da jajircewar Yemi Osinbajo a shekara 63

Bola Tinubu ya yabawa kishi, amana da jajircewar Yemi Osinbajo a shekara 63

Babban Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya koda Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, yayin da kara shekara a Duniya.

Tsohon gwamnan na jihar Legas watau Bola Tinubu, ya fitar da jawabi na musamman a daidai lokacin da Farfesa Yemi Osinbajo ya ke murnar cika shekaru 63 a ban kasa.

A yau Lahadi, 8 ga Watan Maris, 2020, ake murnar zagayowar ranar haihuwar Yemi Osinbajo. An haifi mataimakin shugaban Najeriyar a irin wannan rana ne a shekarar 1957.

Jigon na APC a Kudancin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana Yemi Osinbajo a matsayin zakakurin Masanin shari’a wanda ya tsaya tsayin-daka a kan akidunsa.

Tsohon gwamnan ya fitar da jawabi ne ta bakin Hadiminsa, Tunde Rahman. Wannan jawabi da ya fito daga ofishin Rahman ya shigo hannun Legit.ng ne a jiya Ranar Asabar.

KU KARANTA: NEC: Jam'iyyar APC ta yi shelar wani babban taro na musamman

Bola Tinubu ya yabawa kishi, amana da jajircewar Yemi Osinbajo a shekara 63
Osinbajo ya rike Kwamishina a Gwamnatin Tinubu tsakanin 1999 zuwa 2007
Asali: Twitter

Bola Ahmed Tinubu ya tuna baya inda ya bayyana yadda ya yi aiki da Yemi Osinbajo a lokacin da shi ya ke gwamna a Legas. Osinbajo ya rike Kwamishinan harkar shari’a a lokacin.

Ya ce: “Zan iya tuna yadda mu ka yi aiki tare da kuma wasu wadanda su ka kware wajen kafa tubulin cigaban jihar Legas. Mun yi amfani da shari’a wajen sakewa Legas zani”

“Mafi yawan nasarorin da mu ka samu a kotun koli, su na dauke da tambarin Osinbajo.” ‘Dan siyasar ya ce da Osinbajo gwamnatin Legas ta iya karbo hakkokinta a gaban kotu.

Har ila yau, Tinubu ya yaba da kishi da rike amana da kuma jajircewar Osinbajo. A karshe ya yi masa addu’ar koshin lafiya da samun karfi domin cigaba da bautawa kasarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel