Haraji: Ana binciken Dillalin ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo, Jorge Mendes

Haraji: Ana binciken Dillalin ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo, Jorge Mendes

Mun samu labari daga Jaridun kasashen waje cewa ana binciken dillalin ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo, Jorge Mendes da zargin kin biyan kudin haraji.

Jaridar Daily Star ta bayyana cewa ana zargin Jorge Mendes da laifin damfarar kudi da kin biyan haraji. Wannan ya sa aka fara bibiyar wuraren aikinsa.

Jami’an ‘Yan Sanda sun soma binciken Dilallin ne a boye ba tare an sani ba. Haka zalika kuma ‘Yan Sanda su na binciken wasu Abokan huldar ta sa.

Daga cikin wadanda Jami’an tsaro su ka kai wa samame akwai manyan kungiyar Benfica, Porto da kuma kungiyar Sporting Lisbon da ke kasar Portugal.

Rahotanni sun bayyana cewa Dakarun ‘Yan Sanda sun yi wa gidajen shugabannin kungiyar kwallon kafan Benfica da Porto da kuma Sporting Lisbon ta-tas.

KU KARANTA: Ronaldo ya na son ya koma Real Madrid da ya baro

Ana jin kishin-kishin din cewa ana binciken wasu kamfanonin Jorge Mendez da ke Garuruwan Porto da Lisbon. Ainihin Mista Mendes Mutumin Portugal ne.

Haka zalika Jami’an tsaro sun fara binciken wasu gidajen Attajirin da ke Garin Porto. Wannan duk ya na cikin yunkurin bankado badakar kudin haraji.

‘Yan wasan da ake zargi da laifin kin biyan cikakkun kudin haraji a kasar Turan sun hada da Iker Casillas, Jackson Martinez, Maxi Pereira da Danilo Pereira.

Mendes shi ne Dillalin Tauraron ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo wanda aka taba zargi da irin wannan laifi. Haka zalika ya na da ‘Yan wasa sosai a karkashinsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel