Rikicin APC: Oshiomhole ya garzaya fadar shugaban kasa wurin Buhari
Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC na kasa da wata kotu ta jingine dakatarwar da aka yi masa ranar Laraba, ya garzaya fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ke birnin tarayya, Abuja, da tsakar ranar Alhamis.
Ziyarar ta Oshiomhole na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da cewa ta kwace iko da hedikwatar jam'iyyar APC da ke Abuja.
Rahotonni na nuni da cewa Oshiomole ya shiga ganawar sirri da shugaba Buhari bayan isarsa fadar shugaban bayan karfe 4:00 na yammacin yau, Alhamis, 5 ga watan Maris.
A ranar Alhamis ne wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke jihar Kano ta jingine hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja na dakatar da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adam Oshiomhole, a ranar Laraba.
A hukuncin da kotun ta yanke, mai shari'a, Jastis Lewis Allagoa, ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da rundunar 'yan sanda (NPF) a kan su mayar wa da Oshiomhole jami'an da ke tsaron lafiyarsa domin ya koma ofishinsa.
A ranar Labara ne mai shari'a, Jastis Danlami Senchi, ya bayar umarnin wucin gadi na dakatar da Oshiomhole daga gabatar da kansa a matsayin shugaban APC na kasa.
DUBA WANNAN: Sanatan APC mai ci ya yi Alla wadai da mulkin dimokradiyya, ya yabi mulkin soji
Sa'o'i kadan bayan zartar da hukuncin kotun a ranar Laraba, Oshiomhole ya daukaka kara zuwa wata kotun daukaka kara da ke Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa mai shari'a, Jastis Lewis Allagoa, ne ya yanke hukuncin jingine dakatarwar da aka yi wa Oshiomhole ranar Laraba.
Sai dai, har yanzu ba a samu cikakken rahoto a kan waye ya shigar da kara a kotun Kano dangane da dakatar da Oshiomhole ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng