Oshiomhole: Watakila NEC za ta nada sabon Shugaban Jam’iyya bayan hukuncin kotu

Oshiomhole: Watakila NEC za ta nada sabon Shugaban Jam’iyya bayan hukuncin kotu

Mun samu labari daga wata Jarida cewa majalisar zartarwa watau NEC ta jam’iyyar APC ta na tunanin yadda za ta maye gurbin Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya.

Jaridar ta ce tun a Ranar Laraba wasu gwamnonin jihohin APC su ka fara neman wanda zai canji Adams Oshiomhole wanda kotu ta dakatar, kuma aka hana shi shiga ofishinsa a Abuja.

Ana sa ran cewa za a kira taron NEC na gagagwa, a wannan taro ne za a samu matsaya har a fito da wanda zai cigaba da shugabantar jam’iyya. A halin yanzu APC ba ta da shugaba.

Majiyar ta bayyana cewa akwai yiwuwar manyan jam’iyyar su bukaci Oshiomhole ya yi murabus, sannan sai a nada shugaban jam’iyya na rikon kwarya kafin a kai ga tabbatar da shi.

Sai dai Adams Oshiomhole ta bakin Mai magana da yawunsa, Simon Ebegbulem, ya bayyana cewa ya shigar da kara a kotu, ya na kalubalantar wannan hukunci da aka yanke jiya.

KU KARANTA: Mulkin Soja ya fi farar hula inji Sanatan APC mai ci

Oshiomhole: Watakila NEC za ta nada sabon Shugaban Jam’iyya bayan hukuncin kotu
Ana rade-radin hurowa Oshiomhole wuta ya bar kujerar APC
Asali: UGC

Wadanda su ka kai shugaban jam’iyyar kara gaban kotu sun hada da shugaban APC na jihar Edo da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Yankin Arewa maso gabas da kuma wasu.

A cewar wani daga cikin manyan shugaban jam’iyyar, ya zama dole a kira taron gaggawa a APC idan har ba a janye wannan hukunci da kotu ta yanke na dakatar da Oshiombole ba.

A sakamakon wannan kara, Alkali ya sa jami’an tsaro su hana Adams Oshiomhole shiga ofis ko kuma ya rika yawo da sunan cewa shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa a Najeriya.

Kwanakin baya dama can an yi ta rade-radin wasu gwamnonin APC su na yunkurin tsige Adams Oshiomhole daga kan kujerarsa na shugaban jam’iyya da sunan cewa ya gaza aikinsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel