APC: Mataimakin Oshiomhole ya bayyana jin dadin dakatar da shi, ya bayyana dalilin

APC: Mataimakin Oshiomhole ya bayyana jin dadin dakatar da shi, ya bayyana dalilin

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC reshen arewa maso gabas, Mustapha Salihu, ya ce kadan ya rage shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya haddasa rikici kafin kotu ta sanar da dakatar da shi ranar Laraba.

Da ya ke tsokaci a kan hukuncin da mai shari'a, Jastis Danladi Senchi, ya zartar, Salihu ya bayyana cewa haka kawai Oshiomhole ya umarci kakakin jam'iyyar APC, Malam Lanre Issa Onilu, da ya sanar da sunan daya daga cikin 'yan takara a matsayin sabon sakataren jam'iyyar APC na kasa.

Salihu ya bayyana cewa Oshiomhole ya bayar da umarnin ne ba tare da tuntuba ko yin shawara da kowa ba, lamarin da ya kusa gwara kan shugabanni da mambobin jam'iyyar APC.

A cewar Salihu, dan asalin jihar Adamawa, Oshiomhole yana gudanar da harkokin jam'iyya tamkar a tsarin mulkin sarauta, lamarin da yasa shi da wasu mambobin jam'iyyar 4 suka shigar da kararsa kotu domin ta hana shi bayyana kansa a matsayin shugaba na kasa tunda dai jam'iyyar APC a jihar Ondo ta dakatar da shi tuntuni.

APC: Mataimakin Oshiomhole ya bayyana jin dadin dakatar da shi, ya bayyana dalilin

Oshiomhole
Source: Depositphotos

"Kotu na sanar da cewa an dakatar da shi a wancan lokacin, sai ya kira sakataren yada labaran jam'iyya tare da bashi umarnin ya sanar da manema labarai cewa Bulama ya zama sabon sakataren jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Dan takarar APC ya janye daga zaben maye gurbi da za a yi a Sokoto, ya ce a zabi PDP

"Ya yi gaban kansa ne kawai wajen bayar da umarnin. A zaman mu na karshe ba a cimma matsaya ba a kan waye zai zama sabon sakataren jam'iyya daga cikin jerin masu neman kujerar ba bayan sakataren da aka zaba da farko ya zama gwamna a jihar Yobe," a cewar Salihu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel