Nadin mukamai: Kungiya ta na zargin Gwamnati da nunawa 'Yan Kudu banbamci

Nadin mukamai: Kungiya ta na zargin Gwamnati da nunawa 'Yan Kudu banbamci

Wata kungiya ta ‘Yan kishin kasa a Najeriya, ta yi magana gama da salon nadin mukaman gwamnatin tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke jagoranta.

Wannan kungiya ta yi tir da yadda shugaban kasar ya ke raba mukamai inda ta zargin gwamnatinsa da nunawa mutanen Kudu maso Gabas banbanci da wariya.

Shugaban wannan kungiya da kuma Sakatarensa, Okonkwo James da Isa Pai, su ne su ka yi magana a gaban ‘Yan jarida a cikin farkon makon nan a birnin tarayya Abuja.

Okonkwo James da Isa Pai sun zanta da ‘Yan jarida ne a sakamakon nada Misis Folasade Yemi-Esan da aka yi a matsayin sabuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Idan ba ku manta ba, shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da Yemi-Esan a kujerar shugaban ma’aikatan gwamnatin Najeriya bayan sallamar Winifred Ekanem Oyo-Ita.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya aikawa mutanen Jigawa sakon ta'aziyya

Nadin mukamai: Kungiya ta na zargin Gwamnati da nunawa 'Yan Kudu banbamci

Folasade Yemi-Esan ta canji Winifred Oyo-Ita da ta fito daga Kudu
Source: Twitter

Rahotanni sun ce a dalilin haka wannan kungiya ta ce gwamnatin Buhari ta na ware mutanen Kudu maso Gabas idan aka tashi nada muhimman mukamai maso tsoka.

“A yau babu alamar wani Mutumin Kudu maso Gabas ko wani Ibo da ke jan ragamar wani babban ofis ko kuma rike da wani mukamin siyasa a kasar nan.” Inji James da Pai.

Kungiyar ta kara da cewa: “Ta kai dole mu tambaya cewa, wani laifi Maza da Matan Ibo su ka yi a Najeriya? Yankin su na da manyan kwararrun mutanen da su ka san aiki.”

Okonkwo James ya ce: “Abin da ya kamata Buhari ya yi shi ne ya nada Mutumin Kudu maso Gabashin kasar nan ya rike kujerar shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel