Ana rade-radin Cristiano Ronaldo ya na son ya koma Real Madrid
Jita-jita ta na yawo cewa akwai yiwuwar Cristiano Ronaldo ya bar kungiyarsa ta Juventus, ya tattara ya koma kungiyar Real Madrid da ya bari a shekarar 2018.
Tauraro Cristiano Ronaldo ya dawo Birnin Madrid a Ranar Lahadi inda ya shiga cikin ‘yan kallo na babban wasan El-Clasico da kungiyarsa ta da, ta buga da Barcelona.
Rahotanni sun ce ‘Dan wasan Duniyan ya na da burin komawa kungiyar Real Madrid. Wani na-kusa da Cristiano Ronaldo mai suna Edu Aguirre ya bayyana wannan.
Edu Aguirre ya ce Ronaldo ya na da burin komawa kungiyar Real Madrid da ya bari shekaru kusan biyu da su ka wuce bayan ya kafa irin tarihin da za a dade ba a karya ba.
Aguirre ya bayyana cewa dawowa filin Santiago Bernabeu da Ronaldo ya yi domin ya kalli wasan El-Clasico ya nuna cewa har gobe kungiyar na cikin zuciyar ‘Dan wasan.
KU KARANTA: Cristiano Ronaldo ya kalli wasan El-Clasico a Santiago Bernabeu
A cewar Edu Aguirre: “Na tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo ya na da sha’awar sake dawowa Real Madrid.” Aguirre ya fadawa Gidan talabijin na Chiringuito wannan.
“Ya ji kaunar da ya ke yi wa Madrid a jikinsa lokacin da ya dawo filin wasan Santiago Bernabeu.” Inji Aguirre wanda ya na cikin Na-kusa da ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo.
Ana zargin cewa tabarbarewar alakar Ronaldo da shugaban Real Madrid watau Florentino Perez a karshen zamansa ne ya sa ‘Dan wasan gaban ya koma kungiyar Juventus.
‘Dan wasan na Portugal ya ci kwallaye 450 a Madrid. A makon jiya an ga Ronaldo ya na murna a lokacin da Real ta ci Barcelona, wanda hakan ya tado jita-jitar dawowarsa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng