Sabon tsarin albashi: Kungiyar SSANU ta na tunanin tafiya yajin aiki

Sabon tsarin albashi: Kungiyar SSANU ta na tunanin tafiya yajin aiki

Kungiyar SSANU ta manyan Ma’aikatan Jami’a ta bayyana cewa har yanzu su na kan tsarin tsohon albashi ne a Najeriya duk da karin da gwamnati ta yi tun kwanaki.

Kamar yadda mu ka samu labari, SSANU ta bayyana cewa rashin fara dabbaka sabon tsarin albashi a kan ‘Yan kungiyarta ya jefa su cikin matsin kudi da kuma tattali.

Kungiyar ta ce ba za ta iya bada tabbacin zaman lafiya a makarantun jami’an gwamnatin tarayya muddin aka cigaba da daukar lokacin ba tare da an kara masu albashin ba.

SSANU ta yi wannan jawabi ne a Ranar Litinin ta bakin Mai magana da yawunta, Mista Salaam Abdussobur. A cewarsa an manta da kungiyar a karin albashin da aka yi.

Salaam Abdussobur ya nuna cewa yayin da aka yi wa sauran ma’aikata a kasar karin albashi, har yanzu ba a waiwayi ma’aikatan da ke jami’a wadanda ba su koyarwa ba.

Ga abin da jawabin na Salaam Abdussobur a birnin Abuja ya ke cewa:

KU KARANTA: An hana Ma'aikatan kananan hukumomi karin albashi a Gombe

Sabon tsarin albashi: Kungiyar SSANU ta na tunanin tafiya yajin aiki
Kungiyar SSANU ta ce har yanzu ba ta samu karin albashi ba
Asali: UGC

“Kungiyar manyan Ma’aikatan jami’o’in Najeriya ta koka game da nawan da ake samu wajen dabbaka mata sabon tsarin albashi a cikin makarantun jami’o’i.”

“Batun yarjejeniyar sabon tsarin albashi ya dauki dogon lokacin da ya haura shekaru biyu. Mun dauka cewa da zarar an kammala wannan, za a fara biyanmu.”

“Abin takaicin shi ne, watanni bayan an ci ma matsaya, alamu sun nuna cewa an manta da ma’aikatan jami’a a cikin wannan karin albashi da aka yi.”

“Yayin da sauran ma’aikatan gwamnati su ke morewa sabon tsarin albashi, ma’aikatan jami’a ba su fara shaida wannan kari da aka yi ba tukun.” Inji Abdussabour.

Kungiyar ta ce a sakamakon sai dai su ji labarin karin albashin a makwabta, farashin kaya da su ka tashi bayan an yi karin, ya jawo masu matsin lamba a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel