Tsananin bugu: Malamin ya kashe dalibinsa a makarantar sakandire

Tsananin bugu: Malamin ya kashe dalibinsa a makarantar sakandire

Kelvin Ogheneogaga, dalibin wata makarantar sakandire, Ekiugbo Grammar School, da ke karamar hukumar Ughelli ta arewa a jihar Delta, ya rasa ransa sakamakon dukan da ake zargin malaminsa ya yi masa.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa daliban makarantar sun barke da zanga-zanga a ranar 26 ga watan Fabrairu sakamakon mutuwar dalibin.

Fusatattun daliban sun far wa malamin da ya bugi marigayin, sun lalata ofishin shugaban makarantar tare da jifan motar 'yan sanda.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta bayyana cewa sai da daliban suka sanar da malamin cewa Kelvin bashi da koshin lafiya, sakamakon wani rauni da ya samu a kafarsa, amma duk da haka malamin ya cigaba da bugunsa kamar Allah ya aiko shi.

"Mun roki malamin, mun hada shi da Allah a kan kar ya bugi Kelvin saboda bashi da lafiya amma ya yi burus da mu. Kelvin ya samu rauni a kafarsa kafin malamin ya buge shi; mu na zargin cewa dukan ne ya zama sanadin mutuwarsa," a cewar majiyar.

Tsananin bugu: Malamin ya kashe dalibinsa a makarantar sakandire
Malami yana koyarwa a aji
Asali: Facebook

Isar jami'an 'yan sanda harabar makarantar bata tsorata fusatattun daliban ba ko kadan, hasali ma sun rufe motar 'yan sandan da jifa da duwatsu da kuma sauran makamai masu hatsari da suke rike da su.

Jaridar 'The Nation' ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Delta, Hafiz Inuwa, amma hakan bata samu ba.

DUBA WANNAN: Bidiyon tsiraici: Maryam Booth ta shigar da karar tsohon saurayinta, ta nemi ya biyata N300m

Sai dai, wani babban jami'in dan sanda da ke aiki da ofishin hukumar a Ughelli ya ce, "daliban makarantar sakandire ta 'Ekiugbo Grammar School' sun gudanar da zanga-zanga bayan dalibin makarantar ya mutu sakamakon tsananin bugun da ya sha a wurin malaminsa.

"Malamin ya yi wa dalibin bulala domin hukunta shi a ranar 26 ga watan Fabrairu, bayan dalibin ya koma gida ne sai jikinsa ya rikice, lamarin da yasa aka garzaya da shi zuwa babban asibitin garin Ughelli, inda a nan ne kuma ya mutu.

"Bayan labarin mutuwarsa ya isa makarantar ne sai daliban suka fara zanga-zanga tare da lalata motar makarantar mallakar shugaban makaranta da sauran malamai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng