Ondo: Mataimakin tsohon Gwamna Mimiko da Manyan PDP sun koma APC

Ondo: Mataimakin tsohon Gwamna Mimiko da Manyan PDP sun koma APC

Yayin da zaben gwamnan jihar Ondo ya ke gabatowa, wasu daga cikin ‘Ya ‘yan jam’iyyar PDP da kuma Zenith Labour Party sun sauya-sheka zuwa APC.

An karbi wasu ‘Yan adawa a wajen bikin da ‘Yan jam’iyyar APC su ka shirya domin taya gwamna Rotimi Akeredolu murnar cika shekaru uku a kan mulki.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Lasisi Oluboyo wanda ya rike kujerar mataimakin gwamna a lokacin da Olusegun Mimiko ya ke mulki, ya sauya-sheka.

Haka zalika shugaban jam’iyyar PDP na farko a jihar Ondo, Kanal Samuel Awodeyi mai ritaya da wasu da ake ji da su a jam’iyyar PDP sun bi tafiyar APC.

Sauran wadanda su ka sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki sun hada da Olabisi Johnson da kuma Taye Akinyele, wanda sun taba rike mukamai a jihar.

KU KARANTA: Akeredolu ya na barazanar nada 'Dansa Shugaban ma'aikatan fadar gidan gwamnati

Ondo: Mataimakin tsohon Gwamna Mimiko da Manyan PDP sun koma APC
Tsohon Mataimakin Gwamnan Ondo da wasu 'Yan siyasa sun bi Akeredolu
Asali: Depositphotos

Akwai tsofaffin shugabannin kananan hukumomi shida da su ka bayyana komawarsu cikin jam’iyyar APC a wajen wannan biki da aka yi a Garin Akure.

APC ta ce wadannan ‘Yan siyasa da su ka sauya-sheka sun shigo cikin jam’iyyar APC da Magoya bayansu mutane 10, 000 daga kananan hukumomi 18 na jihar.

Wadanda su ka sauya-shekar sun bayyana cewa irin namijin kokarin da gwamnatin APC ta Oluwarotimi Akeredolu ta ke yi, ya sa su ka dawo cikin APC.

Olabisi Johnson shi ne wanda ya yi magana a madadin sauran sabon shiga APC a wajen bikin. Johnson ya yaba da irin salon mulki mai girma gwamna Akeredolu.

Sai dai jam’iyyar PDP ta bakin shugabanninta, ta bayyana cewa wannan sauyin-sheka bai shafe ta ba. ‘Yan PDP sun ce Magoya bayan ZLP ne su ka koma APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel