Ronaldo ya kalli wasan El-Clasico sakamakon soke wasan Juventus da Inter
Cristiano Ronaldo ya na cikin wadanda su ka kalli wasan El-Clasico tsakanin Real Madrid da Barcelona a jiya Ranar Lahadi, 2 ga Watan Maris 2020 da dare.
Tsohon Tauraron na Real Madrid ya halarci wannan wasa mai zafi da aka buga a filin Santiago Bernabeau na Madrid, inda Barcelona ta sha kashi da ci 2-0.
Ronaldo ya zo Sifen ne a sakamakon dakatar da wasan kungiyarsa ta Juventus da Inter Milan. An dage wasan ne a a dalilin barkewar cutar Coronavirus a kasar.
Rahotanni su na zuwa mana cewa wannan cuta ta yi kamari a kasar Italiya inda Ronaldo ya ke taka leda. Yanzu haka akalla mutane 30 ne su ka mutu a dalilin cutar.
C. Ronaldo wanda ya buga wasannin El-Clasico 30 daga shekarar 2009 zuwa 2018 ya yi murna da nasarar da tsohuwar kulob dinsa ta samu a kan Abokan gabanta.
KU KARANTA: Budurwar Ronaldo ta na yawo da aworwaron miliyoyin kudi
Fitaccen ‘Dan wasan gaban Duniyan ya zauna ne a wurin da ake ajiye manyan baki na VIP a cikin filin wasan, inda aka ga ya na murna bayan Real ta ci kwallo.
A minti na 71 ne Matashin ‘Dan wasa Vinicius Jr. ya zura kwallon farko, ya kuma yi irin salon murnar da Ronaldo ya kan yi idan ya ci kwallo a lokacin ya na Real.
A daf da za a tashi wasan ne Mariano Diaz ya jefa kwallo na biyu bayan ya karkato daga gefen dama. Hakan na nufin Baki Real Madrid su ka yi nasara da ci 2-0.
Abin da nasarar ta ke nufi shi ne Real ta dare saman teburin La-liga. A lokacin da Cristiano Ronaldo ya ke bugawa Real Madrid, ya ci kwallaye 18 a wasan El-Clasico.
Da wannan tafiya ta kilomita 1300 da Ronaldo ya yi takanas tun daga Turin zuwa Garin Madrid ya nuna cewa har yanzu kungiyar da ya ci wa kwallo 450 ta na ransa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng