Babban bankin Najeriya ta ce za ta bi ta kan Attajiran da ake bi tarin bashi

Babban bankin Najeriya ta ce za ta bi ta kan Attajiran da ake bi tarin bashi

Babban bankin Najeriya watau CBN ta ce za ta yi maganin mutanen da ake bi tarin bashin kudi a bankuna amma su ka ki biyan kudin babu gaira babu dalili.

CBN ta bayyana cewa za ta fara karbe gidaje da kadarori da kuma jiragen hawan wadanda su ka ki biyan bankuna bashin da aka dade ana binsu a Najeriya.

Gwamnan CBN ya yi wannan barazana ne a karshen makon nan bayan da shi da wasu manyan gwamnati su ka ziyarci matatan danyen man Aliko Dangote.

Kamar yadda Jaridar This Day ta bayyana, gwamnan na CBN ya ce babban banki zai cigaba da bada bashi ga wadanda su ke biyan aron kudinsu a kan kari.

Da ya ke jawabi a Ijebu-Lekki Ranar Asabar, Emefiele ya gargadi manyan kasar da cewa: “Babban bankin CBN ba zai sake bari a bada aron kudin da ba za a biya ba.

KU KARANTA: Buba Galadima ya yi magana bayan hukuma ta karbe gidansa

Babban bankin Najeriya ta ce za ta bi ta kan Attajiran da ake bi tarin bashi
CBN ta ce za ta bi ta kan masu cin bashi su ki biya a Najeriya.
Asali: Twitter

Godwin Emefiele ya ce: “Idan ka na hawa jirgin sama ne, za mu karbe jiragen, sai ku koma tuka kekuna. A lokacin za mu tabbatar cewa ka biya bashin ka.”

“Ba za ka karbi aron kudi, sannan ka rika yawo a jiragen sama ba. Za mu taso ka a gaba. Dole sai ka biya wadannan bashi da ke kan ka.” Inji Gwamnan.

Har ila yau, gwamnan na CBN, Mista Emefiele ya yabawa irin kokarin Dangote na kafa matatar danyen man da zai sa Najeriya ta daina shigo da fetur.

Gwamnan babban bankin kasar ya yi hasashen cewa matatar Dangote za ta dauki mutane kusan 70, 000 aiki. Wannan namijin aiki zai ci fam Dala biliyan 15.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel