Coronavirus: An dakatad da duk wani Sallar Juma’a da Khamsu-Salawati a kasar Iran

Coronavirus: An dakatad da duk wani Sallar Juma’a da Khamsu-Salawati a kasar Iran

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Iran ta yi sanarwa ranar Alhamis cewa an dauki wasu sabbin matakan dakile yaduwar cutar Coronavirus da ta addabi kasar cikin makon nan.

Daya daga cikin matakan shine dakatad da Sallar Juma’a har ila ma sha’a llahu.

Ma’aikatar ta bayyana cewa an haramta duk wani taron baja koli, khamsu-salawati, gidajen Sinima, bukukuwa, jana’iza, i’itikafi da duk wani gangami a kasar.

Shugaban sashen yada labaran ma’aikatar, Kianush Jahanpur, ya ce an kara yawan cibiyoyin gwajin cutar Coronavirus daga biyu zuwa bakwai, kuma za’a kara zuwa 15 kafin karshen makon nan, kuma 22 a makon gobe.

Hukumomin kasar Iran sun sanar a ranar Laraba cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar ya tashi zuwa 19 kuma mutane 139 suka kamu.

Bugu da kari, kasar Iran ta kulle dukkan makarantu, jami’o’i, cibiyoyin Ilimi a garin Qom da Arak.

Coronavirus: An dakatad da duk wani Sallar Juma’a da Khamsu-Salawati a kasar Iran
Coronavirus: An dakatad da duk wani Sallar Juma’a da Khamsu-Salawati a kasar Iran
Asali: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa Mataimakiyar shugabar kasar Iran kan harkakokin mata da Iyali, Masoumeh Ebtekar, ta kamu da cutar Coronavirus da ta addabi duniya, jaridar kasar ta ruwaito.

Masoumeh Ebtekar ce mambar majalisar zartarwar kasa ta farko da zai kamu da cutar tun lokacin da ta bulla a Iran.

A yau, shugaban kwamitin harkokin wajen Iran na majalisar dokokin kasar, Mojitaba Zolnour, ya bayyana a wani faifan bidiyo cewa shi ma ya kamu da cutar ta Coronavirus.

Hakazalika wani dan majalisa, Mahmoud Sadeghi da mataimakin ministan kiwon lafiyar kasar, Iraj Harichi, sun tabbata da kamuwa da muguwar cutar.

Bugu da kari, gidan talabijin kasar ta sanar a yau Alhamis cewa babban Malami Hadi Khosroshahi, ya mutu sanadiyar kamuwa da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel