'Yan agaji sun kashe 'yan bindiga 17 a Katsina, fararen hula 4 sun mutu

'Yan agaji sun kashe 'yan bindiga 17 a Katsina, fararen hula 4 sun mutu

Wasu mutane hudu sun rasa ransu yayin wani hari da 'yan bindiga suka kai kauyen Gurbi a karamar hukumar Kankara da ke jihar Katsina.

A cikin wani jawabi da rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta fitar ta bakin kakakinta, DSP Gambo Isah, ta bayyana cewa an kai harin ne da tsakar ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa 'yan bindigar sun raunata karin wasu mutane uku tare da yunkurin sace dabbobi kafin su fuskanci tirjiya daga 'yan kungiyar sa kai, watau kungiyar 'bijilante'.

Mutane hudun da suka rasa ransu sun hada da; Alhaji Sanusi 'Yar Bakare, Akili Isuhu daga Bawa Mai Ruwa,Nana Husaini Unguwar Farin Duste, da Muntari Sama'ila daga gidan Korau.

'Yan agaji sun kashe 'yan bindiga 17 a Katsina, fararen hula 4 sun mutu
Kauyen jihar Katsina
Asali: Facebook

Isah ya bayyana cewa kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina, Sanusi Buba, ya umarci DPO din karamar hukumar Kankara ya jagoranci 'yan sandan tawagar 'Puff Adder' da 'yan bijilanti zuwa kauyen bayan samun kiran 'kan ta kwana' a kan abinda ke faruwa a kauyen.

DUBA WANNAN: Hukuncin kotu: An kashe mayakan kungiyar Boko Haram 10 ta hanyar bude musu wuta

Ya kara da cewa rundunar 'yan agajin da jami'an 'yan sanda ta fafata da 'yan bindigar, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe 17 daga cikinsu yayin da wasu suka gudu da raunukan harbi a jikinsu.

"Tawagarmu ta yi nasarar kashe 17 daga cikin 'yan bindigar tare da samun nasarar kwace shanu 80, tumaki 108, da Jaki guda daya," a cewar jawabin.

A cewar kakakin, jami'an 'yan sanda sun kewaye dazukan gefen kauyen domin tabbatar da cewa 'yan bindigar da suka gudu basu samu tsira ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel