Adamawa: Emmanuel Bello ya na so a binciki abin da ya faru a harin Garkida

Adamawa: Emmanuel Bello ya na so a binciki abin da ya faru a harin Garkida

Tsohon ‘dan takarar gwamnan jihar Adamawa, Emmanuel Bello, ya bukaci ayi bincike game da lamarin da ya auku a lokacin da ‘Yan Boko Haram su ka kai hari a jihar.

Idan ba ku manta ba, a makon da ya gabata, wasu ‘Yan ta’addan Boko Haram sun yi mugun ta’adi a Garin Garkida da ke cikin karamar hukumar Gombi a jihar Adamawa.

Emmanuel Bello wanda ya nemi kujerar gwamnan Adamawa a karkashin jam’iyyar SDP a zaben 2019, ya zargi Sojoji da janye Dakarunsu a daidai lokacin da za a kai harin.

A wani jawabi da Mista Emmanuel Bello ya fitar a Ranar Laraba, 26 ga Watan Fubrairun 2020, ya ce ya kamata gwamnati ta yi tunanin biyan diyya ga wadanda abin ya shafa.

“Don haka ina kira ga gwamnatin tarayya ta binciki mummunan harin Ranar 21 ga Watan Fubrairu, a Garkida domin gano abin da ya jawo saukin shigan ‘Yan ta’adda.”

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi babban rashi a harin Garkida

Jawabin ‘Dan siyasar na Adamawa ya kara da cewa: “Gwamnatoci a kowane bangare su yi tunanin biyan kudin diyya ga Mazauna Garin (Garkida) da aka yi wa barna a harin.”

Bello ya na ganin cewa zamewan da Rundunar Sojoji su ka yi daga Garkida ne ya ba ‘Yan ta’adda daman shigo Garin su yi barna kamar yadda Hukamar dillacin labarai ta bayyana.

Emmanuel Bello ya koka game da sababbin hare-haren da ‘Yan ta’addan su ke kai wa Bayin Allah a Yankin. A karshe, ya yi kira ga Jami’an tsaro su canza dabaru domin su yi nasara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel