‘Yan Majalisa su na kokarin kawo kudirin da zai yi masu katanga daga bincike
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa kudirin da ke kokarin kare shugabannin majalisar tarayya daga bincike, ya tsallake matakin farki a Najeriya.
Wannan kudiri da Honarabul Odebunmi Olusegun ya gabatar ya na yunkurin yi wa sashe na 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya wasu ‘yan garambawul.
Idan har an yi nasarar amincewa da wannan kudiri, za ayi wa dokar kasa kwaskwarima ta yadda zai zama ba za a iya binciken shugaban majalisar tarayya ba.
‘Dan majalisar mai wakiltar Yankin jihar Oyo, Odebunmi Olusegun, ya ce ya kawo wannan kudiri ne domin shugabannin majalisa su iya yin aikinsu da kyau.
A cewar Odebunmi Olusegun, idan har aka yi na’am da wannan kudiri, shugabannin majalisar tarayya za su ji dadin aiki ba tare da yin wani rangwame ba.
KU KARANTA: Majalisa ta ba Janar Tukur Buratai umarni ya bude sabon sansanin Soji
Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Honarabul Alhassan Ado Doguwa, ya tofa albarkacin bakinsa a lokacin da aka gabatar da kudirin a jiya.
Doguwa ya ce Kakakin majalisa ba ya bukatar kariyar a karon-kansa, sai dai don a tsare majalisa. “Ka da mu ki yin magana game da abin da ya shafi majalisa.”
“Majalisa ce kashin-bayan damukaradiyya, don haka idan doka za ta kare shugaban kasa da gwamnoni, ina ga shugabannnin majalisa don su yi aikinsu?”
Honarabul Toby Okechukwu mai wakiltar jihar Enugu a karkashin PDP ya yi magana game da yadda aka matsawa shugaban majalisar dattawa da bincike a baya.
Irinsu Ndudi Elumelu, Bob Solomon, da Sergius Ogun sun nuna adawa ga wannan kudiri, su ka ce kashe-kashen da ake yi ya kamata a damu da su ba wannan aiki ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng