Bayelsa: Ana kokarin sauya takardun bautar-kasan Mataimakin Gwamna - Nabena

Bayelsa: Ana kokarin sauya takardun bautar-kasan Mataimakin Gwamna - Nabena

APC ta ce ta gano shirin da shirin da PDP ta ke yi a Bayelsa, inda ake kokarin canza takardun bogin da mataimakin gwamna Lawrence Ewhrudjakpo, ya gabatar gaban INEC.

Jam’iyyar APC ta ce PDP ta na yunkurin canza takardun shaidar bautar kasan da Lawrence Ewhrudjakpo ya gabatar a lokacin da ya shiga takarar mataimakin gwamnan jihar.

A cewar Sakataren yada labarai na APC, Yekini Nabena, Lawrence Ewhrudjakpo ya mikawa INEC satifiket din NYSC na bogi ne, wanda su yanzu haka su na da duk takardun na sa.

Mista Yekini Nabena ya ce mataimakin gwamnan na PDP ya na neman yadda zai canza takardun da ya gabatar a ofishin INEC, inda ya yi kira ga hukumar zaben da ta hana ayi hakan.

Nabena wanda ya ke magana a madadin jam’iyyar APC ya shaidawa ‘Yan jarida wannan ne a lokacin da ya zanta da su a Ranar Lahadi, ya ce su na dalabarin kullen-kullen PDP.

Jam’iyyar APC mai adawa a jihar Bayelsa, ta roki hukumomin INEC da NYSC da cewa ka da ‘Yan PDP su tursasa masu canza takardun ‘Dan takarar da aka riga aka gabatar tun farko.

KU KARANTA: Kujerar Gwamnan Bayelsa za ta koma hannun APC - Ministan Buhari

Bayelsa: Ana kokarin sauya takardun bautar-kasan Mataimakin Gwamna - Nabena
Yekini Nabena ya ce Lawrence Ewhrudjakpo ya na aiki da takardun bogi
Asali: UGC

Mista Nabena ya shaidawa Duniya cewa su na sane da zargin amfani da takardun karyar da ke kan wuyan sabon mataimakin gwamnan, wanda yanzu ya ke kokarin bada cin hanci.

“Bayanin da mu ke samu shi ne Sanata Lawrence Oborawharievwo Ewhrudjakpo ya dumfari INEC da NYSC ya ba su cin hanci saboda a sauya takardun bogin da ya gabatar.” Inji Nabena.

“Mun riga mun samu ainihin takardun bogin shaidar NYSC da mataimakin gwamnan ya mikawa INEC, ina kira ga hukumar ta bi a hankali, ta guji karbar cin hanci ta canza takardun.”

Kafin Ewhrudjakpo ya zama mataimakin gwamnan jihar Bayelsa a Ranar 14 ga Watan Fubrairun 2020, shi ne wanda ya ke wakiltar Yankin Bayelsa ta Yamma a majalisar dattawa.

APC ta na kokarin bin duk wata hanya da za ta iya domin ganin kotu ta karbe mulki daga hannun jam’iyyar PDP, a sakamakon mikawa Douye Diri nasara da aka yi bayan ya fadi zabe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng