Yan sanda sun kashe yan fashi 5 a musayar wuta da suka yi a Katsina

Yan sanda sun kashe yan fashi 5 a musayar wuta da suka yi a Katsina

- Rundunar yan sandan jahar Katsina a yammacin ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu ta baje gawawwakin yan bindigar da ta kashe a yayin wani arangama a Maraba Kankara

- An tattaro cewa yan fashin sun addabi al’umman kananan hukumomin Malumfashi, Faskari, Dandume, Bakori, Kankara da Sabuwa da ke jahar, harma da jihohin da ke makwabtaka da jahar da suka hada da Kano da Zamfara

- Kwamishinan yan sandan jahar, Sanusi Buba ya ce an gano bindigogi AK47 guda uku tare da mujalla hudu cike da alburusai 94

Rundunar yan sandan jahar Katsina a yammacin ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu ta baje gawawwakin yan bindigar da ta kashe a yayin wani arangama a Maraba Kankara da ke karamar hukumar Kankara na jahar.

Kwamishinan yan sandan jahar, Sanusi Buba, ya fada wa manema labarai cewa gawurtattun yan fashin sun addabi al’umman kananan hukumomin Malumfashi, Faskari, Dandume, Bakori, Kankara da Sabuwa da ke jahar, harma da jihohin da ke makwabtaka da jahar da suka hada da Kano da Zamfara.

Ya ce: “Ta cika da yan ta’addan lokacin da aka hade dasu a hanyar Maraba Kankara inda suke a hanyarsu ta zuwa satar mutane da kuma fashi da makami a wani waje a karamar hukumar Gwarzo da ke jahar Kano.”

CP Sanusi ya kara da cewa a yayin da ake masu tambayoyi an gano bindigogi AK47 guda uku tare da mujalla hudu cike da alburusai 94 sannan cewa masu laifin sun tona cewa suna da Karin makamai ciki harda AK47 guda biyu da suka boye a Mararaba Maigoro.

Yan sanda sun kashe yan fashi 5 a musayar wuta da suka yi a Katsina
Yan sanda sun kashe yan fashi 5 a musayar wuta da suka yi a Katsina
Asali: UGC

Kwamishinan yan sandan ya ce an bude wa tawagar wuta sannan suka fafata da yan bindigar, lokacin da Shugaban masu yaki da fashi da makami ya jagoranci wata tawagar jami’ai don kwaso wadannan makaman.

KU KARANTA KUMA: An kone 'yan 'yahoo' biyu, wata bokanya da mai garkuwa da mutane

Ya ce: “A yayin tafiyar, tawagar sun mayar da martani sannan suka dakile harin wanda ya yi sanadiyar kashe dukkanin yan fashin su biyar wadanda aka baje kolin gawarsu.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel