Yau Alkali zai yankewa Olisha Metuh da hukumar EFCC hukunci a kotun Abuja

Yau Alkali zai yankewa Olisha Metuh da hukumar EFCC hukunci a kotun Abuja

Babban kotun tarayya da ke Garin Abuja, zai yanke hukuncin karshe a shari’ar da ake yi da tsohon Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP, Mista Olisah Metuh.

Ana zargin Olisah Metuh da karbar kudi daga hannun Sambo Dasuki a lokacin ya na matsayin Mai bada shawara a kan harkar tsaro a gwamnatin Goodluck Jonathan.

Ana zargin cewa Olisah Metuh ya karkatar da wadannan kudi da aka ba shi da sunan sayen kudin makaman yaki. Naira miliyan 400 ake zargin Metuh ya lamushe.

Alkali mai shari’a, Okon E. Abang, ya ce a yau Ranar 25 ga Watan Fubrairun 2020, zai yanke hukunci, bayan ya saurari bayanin karshe daga bakin kowane bangare.

Olisah Metuh ta bakin Lauyansa, Abel Ozioko, ya hakikance a kan cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya amince a fitar masa da wadannan makudan kudi.

KU KARANTA: Metuh ya bayyana yadda ya samu N400m a gwamnatin PDP

Yau Alkali zai yankewa Olisha Metuh da hukumar EFCC hukunci a kotun Abuja
EFCC ta na zargin Olisha Metuh da karkatar da kudin makamai
Asali: UGC

Lauyan da ke kare wanda ake tuhuma, ya ce an fitar da kudin daga hannun tsohon Mai bada shawara kan harkar tsaro watau Sambo Dasuki ne bayan an bi doka.

A cewar Lauyan Metuh, an yi amfani da wadannan kudi ne domin shaidawa Duniya irin ayyukan da gwamnatin PDP ta Goodluck Jonathan ta ke yi a wancan lokaci.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta ce an sabawa dokar kasa wajen raba wannan kudin makamai da sun kai Dala miliyan 2.

Kusan shekaru hudu aka dauka ana kai-kawo tsakanin hukumar EFCC da tsohon Jami’in na jam’iyyar PDP a kotu. An jima kadan kotu za ta bayyana mai gaskiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel