A sake yi wa tsarin tsaro sabon kallo a kasar nan – Inji Aisha Buhari

A sake yi wa tsarin tsaro sabon kallo a kasar nan – Inji Aisha Buhari

A jiya, Litinin, Uwargidar shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta yi magana game da sha’anin tsaro a Najeriya, bayan an gayyace ta wani taro a Kaduna.

Mai girma Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta bukaci a samu hadin-kai tsakanin dukkanin bangarorin tsaron Najeriya, tare da kira a sake yi wa sha’anin tsaron wani kallo.

Aisha Muhammadu Buhari a jawabin na ta, ta bukaci a kara yi wa yadda tsarin tsaro ya ke wani kallo da idanunan basira domin a kawo karshen matsalar ta’addanci a fadin kasar.

Mai dakin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi wannan magana ne a wajen taron da aka shirya kan sha’anin tsaro a Makarantar koyon aikin Sojin Najeriya na NDA a Kaduna.

Uwargidar shugaban ta nuna cewa matsalar rashin tsaro ne babban abin da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya, don haka ta bada shawarar a tashi tsaye kafin abubuwa su yi kamari.

KU KARANTA: Abubuwan da za su sa mu buda iyakoki Najeriya - Buhari

A sake yi wa tsarin tsaro sabon kallo a kasar nan – Inji Aisha Buhari
Aisha Muhammadu Buhari ta yi kira ga Iyaye da Gwamnati
Asali: UGC

Buhari ta ce: “Sha’anin tsaro shi ne babban kalubalen Najeriya har yanzu, lokaci ya kawo da za a nemi sababbin dabaru, idan ba a bi sannu ba, abubuwa za su kara yin muni a Najeriya.”

Hajiya Buhari ta bukaci ‘Yan Najeriya su zama masu sa-ido, tare ba Jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen shawo kan matsalar rashin tsaron da ake fuskanta a halin yanzu.

“Masu laifi su na cikin mutanen al’umma, kuma su na zama ne a cikinmu, Iyaye su na da hakkin ganin sun yi kokarin bada tarbiya domin cigaban ‘Ya ‘yanmu.” Inji Hajiya Aisha Buhari.

Har ila yau, Matar shugaban kasar ta bada shawara ga gwamnati ta maida hankali kan hakkoki da walwalar Jami’an tsaro domin Sojoji su iya sauke duk nauye-nauyen da ke kansu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel