Mai dokar barci ya buge da gyangyadi: An kama Dansanda da laifin sata da garkuwa da mutane

Mai dokar barci ya buge da gyangyadi: An kama Dansanda da laifin sata da garkuwa da mutane

Wannan shi ne ana zaton wuta a makera, sai aka tsinceta a masaka, jami’an tsaro sun samu nasarar kama wani jami’in Dansanda tare da yan gungunsa wasu mutane biyar da suka yi kaurin suna wajen sata tare da garkuwa da mutane a garin Calabar, jahar Cross Rivers.

Jaridar Punch ta ruwaito jami’an rundunar yaki da miyagun laifuka a jahar Cross Rivers dake aikin “Operation Skolombo” ne suka samu nasarar kama Dansandan da yaransa 5 a ranar Lahadi, 23 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: Azumin jama’an Borno ya fara aiki: Mayakan ISWAP sun kashe kwamandojinsu guda 3

Majiyarmu ta bayyana cewa a yanzu haka ana rike da Dansandan a barikin Sojoji na Eburutu dake cikin garin Calabar, kuma rahotanni sun tabbatar da ya mallaki manyan kadarori da dama a cikin garin Calabar.

Sai dai da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Cross Rivers, DSP Irene Ugbo don jin ta bakinta game da kamen, sai ta ce: “Ba ni da masaniya, zuwa yanzu dai ban ji wani abu ba, amm zan bincika.”

A wani labarin kuma, daga dukkan alamu, Allah Ya karbi azumin da miliyoyin al’ummar jahar Borno da ma wadanda ba yan jahar ba suka yi a ranar Litinin, 24 ga watan Feburairu, kamar yadda gwamnan jahar Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukata domin neman Allah Ya kawo zaman lafiya a jahar.

Shahararren masani dangane da kungiyar Boko Haram, Audu Bulama Bukarti ne ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa rahotanni tabbatattu sun bayyana mayakan kungiyar ta’addanci na ISWAP, wani bangare na Boko Haram sun kashe manyan jagororinsu guda uku.

Daga cikin manyan kwamandojin da rahotanni suka bayyana cewa mabiyansu sun kashesu a ranar Litinin, 24 ga watan Feburairu akwai shugaban kungiyar, Idris Al-Barnawa, Abu Maryam da Abu Zainab, kwamandoji biyu da suka yi ma Shekau bore a 2016.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel