Neman mafita: 'Yan Kannywood sun dukufa addu'o'i da azumi

Neman mafita: 'Yan Kannywood sun dukufa addu'o'i da azumi

Biyo bayan tabarbarewar lamura a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wani kwamitin da yan wasan suka kafa ya dauki aniyar yin gagarumin gangami na addu’o’i tare da azumi.

Hakan na daga cikin kokarin kwamitin na ceto masana’antar daga cikin kalubalen da ta ke fuskanta.

Babban jarumi Misbahu M. Ahmad da Salisu Officer ne suka kafa wannan kwamitin na addu’an, Mujjalar Fim ya ruwaito.

A yayin da ya ke bayyana wannan aniyar, Misbahu ya yi kira ga yan fim baki daya da su samu lokaci ta Juma’a su yi addu’o’in samun mafita daga fitittinun da su ka mamaye masana’antar.

Neman mafita: 'Yan Kannywood sun dukufa addu'o'i da azumi
Neman mafita: 'Yan Kannywood sun dukufa addu'o'i da azumi
Asali: Instagram

Misbahu ya yi kiran ne a cikin Wani sakon murya da ya dauka tare da tura shi kungiyar masana’antar da ke soshiyal midiya kamar yadda majiyarmu ta bayyana.

'Yan fim da dama sun yi na'am da wannan shawara da Misbahu ya kawo.

Daya daga cikin su, furodusa Hassan Zain Ahmad, ya bada sanarwa cewa a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu, 2020 za su buƙaci dukkan mutanen da su ke cikin wannan masana’anta da su ɗauki azumi tare da niyya a kan samun taimakon Allah da samun mafita da ci-gaba a cikin masana’antar ta Kannywood.

KU KARANTA KUMA: Mawaki Nazifi Asnanic ya shiga sahun fitattun mutanen 10 a jahar Kano

Ya ce: "In Allah ya yarda, ranar Litinin za mu tashi da niyya a kan mu yi wannan azumi.

"Ya'yan mu da matan mu da iyayen mu da dukkannin masoyan mu za mu tashi da wannan addu'ar a kan Allah ya kawo mafita a Kannywood. Ubangiji Allah ya taimake mu.

"Sannan kuma za mu yi yanka, za mu yi sadaka, da dukkannin abin da ya sauwaka."

A baya mun ji cewa Shugaban kungiyar masu shirya finafinai ta kasa (MOPPAN), Dakta Ahmad Muhammad Sarari, ya bukaci daukacin yan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, da su tashi tsaye su dukufa wajen yin addu’a kan Allah ya ceto masana’antar daga halin da ta ke ciki.

An tattaro cewa ya yi wannan kiran ne sakamakon ganin yadda masana’antar ta shiga cikin rudani a yan kwanakin bayan nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng