Babu laifi don an nemi a tsige manyan Sojojin Najeriya – Inji kungiyar NBA

Babu laifi don an nemi a tsige manyan Sojojin Najeriya – Inji kungiyar NBA

Mun ji labari cewa kungiyar NBA ta Lauyoyin Najeriya, ta ce babu laifi game da kukan da mutane su ke ta faman yi na cewa ya kamata a sauke hafsun sojojin kasar.

Kungiyar NBA ta ce a yanzu da sha’anin tsaro ya ke tabarbarewa, za a yi fahimtar abin da ya sa wasu ke rokon a sauke manyan sojojin Najeriya, a maye gurbinsu da wasu.

Sakataren yada labarai na kungiyar NBA, Kunle Edun, ya bayyana wannan a lokacin da ‘Yan jarida su ka yi masa tambaya a Ranar Lahadi, 24 ga Watan Fubrairun 2020.

Kunle Edun ya ce ya kamata shugabanni su rika sauraron kukan da jama’a su ke yi. Edun ya ce: “NBA ta damu sosai game da halin rashin tsaron da ake ciki a Najeriya.”

Jawabin ya ce: “Majalisar zartarwa ta kungiyar NBA ta fitar da matsaya sau da-dama ta na kiran gwamnatin tarayya ta yi kokari wajen magance matsalar rashin tsaro.”

KU KARANTA: Buhari ya gano wasu na neman yin zanga-zanga domin a sauke Buratai dsr

Babu laifi don an nemi a tsige manyan Sojojin Najeriya – Inji kungiyar NBA
Kungiyar NBA ta ce rashin tsaro ya yawaita a Najeriya
Asali: UGC

“Za a iya ganin dalilin da ya sa (ake kiran tsige Hafsun Sojoji), saboda yawan kashe-kashen da ake fama da shi da barnar dukiya a sakamakon harin ‘Yan bindiga da Miyagu.”

“A kwanan nan, wasu Miyagu su ka shiga Uwheru, su ka kai hari, su ka kashe mutane takwas. A karamar hukumar Batsari a Katsina, ‘Yan bindiga sun kashe mutane 30.”

“Duk an yi wannan ne a makon jiya, kuma ba iyakar ta’adin ke nan ba. Kowa ya san cewa shugaban kasa Buhari ya nada Hafsun sojojin, kuma shi su ke yi wa aiki.”

“Mulkin farar hula ake yi a Najeriya, zai yi kyau shugabanni su rika sauraron jama’a. A matsayin shugabanni, mulkinku ya rataya ne a kan Talakawan da su ka ba ku amana.”

Ganin kashe-kashe ya yawaita, Edun ya ce: “Idan gwamnati ba ta yin abin da ya dace a wannan bangare, sai ta canza shugabannin sojoji, ta kawo sababbin tsare-tsare.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel