Babu sabuwar doka da aka sa wajen waya da hawa dandalin sada zumunta – Gwamnati

Babu sabuwar doka da aka sa wajen waya da hawa dandalin sada zumunta – Gwamnati

Gwamnatin tarayya ta ce babu wata doka da aka kawo domin sa-ido a kan wayoyi da sakonnin da jama’a su ke aikawa da wayoyin salularsu kamar yadda ake ta rade-radi.

Ministan Ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ya karyata rahotannin da ke yawo na cewa ‘Daga gobe’ za a fara lura da abubuwan da jama’a su ke yi a wayoyin tarho.

Mai girma Ministan ya yi wannan jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun bakinsa, Uwa Suleiman. Hadimar ta fitar da jawabi ne a Ranar Lahadi, 23 ga Fubrairun 2020.

Uwa Suleiman ta ce: “Hankalin Mai girma Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya zo ga wani sakon karya da ake ta yadawa da sunansa.”

“Labarin bogin ya na cewa daga yanzu Ma’aikatar kasar ta na lura da duk wata na’ura, inda za a rika daukar waya, tare da bibiyar sakonnin ake aikawa a zaurukan sadarwa.”

KU KARANTA: Amurka ta tona satar da Gwamnatin Buhari ta ke neman yi - PDP

Babu sabuwar doka da aka sa wajen waya da hawa dandalin sada zumunta – Gwamnati
Isa Ali Pantami ya ce gwamnati ba ta sa-ido kan wayoyin salula
Asali: UGC

“Wannan mugun sako ya kai ga hana mutane yada sakonni ko bidiyoyi da ke dauke da manufar siyasa ko addini, kamar dai yin hakan laifi ne da har zai kai ga a kama mutum.”

A wannan rahoton da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, an ja-kunnen jama’a da cewa su bi a hankali game da abubuwan da su ke yi wayoyin su domin idon gwamnati na nan kar.

Jawabin ya kare da cewa: “Ministan ya na kira ga daukacin ‘Yan Najeriya su yi watsi da furofaganda da aka shirya domin a tsoratar da ‘Yan Najeriya tare da kawo rudani.”

Sai dai akwai yunkurin da ake yi a majalisa na ganin an yi maganin masu yada labaran karya wadanda ka iya tada rigima. Wasu su na ganin akwai lauje cikin nadi a wannan shiri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel