Mu koma ga Allah don ceto Kannywood -Shugaban MOPPAN
Shugaban kungiyar masu shirya finafinai ta kasa (MOPPAN), Dakta Ahmad Muhammad Sarari, ya bukaci daukacin yan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, da su tashi tsaye su dukufa wajen yin addu’a kan Allah ya ceto masana’antar daga halin da ta ke ciki, Mujallar Fim ta ruwaito.
An tattaro cewa ya yi wannan kiran ne sakamakon ganin yadda masana’antar ta shiga cikin rudani a yan kwanakin bayan nan.
A wata takarda mai dauke da kwanan wata 20 ga Fabarairu, 2020, wadda sakataren yada labarai na MOPPAN, Malam Al-Amin Ciroma, ya sanya wa hannu, an ruwaito Dakta Sararu ya na cewa: "Lokaci ya yi da kowanne mai kishin masana'antar zai fito ya mara wa dukkan shirye- shirye da aka yi na samun ci-gaba.
"Komawa ga Allah gami da kudirin alheri su na daga cikin abin da ya kamata mu yi, domin su na daga cikin hanyoyin samar da nasarori a cikin kowanne lamarin."
Sarari ya yi tsokaci kan taron addu'a da aka ce 'yan fim za su yi a ranar Litinin mai zuwa, ya ce abu ne mai muhimmanci 'yan fim su koma ga Allah.
KU KARANTA KUMA: Jabun kudi: Kotu ta yanke wa Hadiza Adamu da sauran wasu mutane 3 hukuncin daurin shekara 60
"Kuma taron addu'ar tamu ya zamo ba wani bangare na siyasa ko neman ganin bayan wani ba, kawai mu sanya cigaban masana'antar a gaba, domin kuwa ta haka ne za mu tsamo kan mu daga halin da mu ke ciki a yanzu."
Daga karshe ya yi fatan samun nasara, da kuma fatan yin taron addu'ar cikin tsarkakakkiyar zuciya.
A wani labarin kuma, mun ji cewa wani bincike da aka gudanar ya zakulo shahararren mawakin nan na Kannywood da bukukuwa, Mallam Nazifi Asnanic daga cikin fitattun mutane 10 a jahar Kano.
A bisa ga binciken wanda jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram na @nazifiasnanic ya nuna cewa mawakin ne na tara cikin sahun fitattun mutanen 10 a jahar Kano.
An tattaro cewa Nazifi ya shiga sahun wadannan mutane saboda gudumuwarsa a harkar nishadantarwa da taka rawa a fina-finan hausa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng