Amarya ta yafe sadakin aurenta, amma ta ce ango yayi mata alkawarin babu shi babu kara mata kishiya

Amarya ta yafe sadakin aurenta, amma ta ce ango yayi mata alkawarin babu shi babu kara mata kishiya

- Wata mata ganau ba jiyau ba mai suna Aishat Busari ta bada labarin yadda wata amarya ta ki karbar sadaki har sai da ango yayi mata alkawari

- A addinin Musulunci, ba dole bane a ba mace sadakinta a matsayin kudi ba. Sadaki na iya zama a wani nau’i na daban da ba kudi ba

- Amarya Fatima Babawale kuwa ta bukaci angonta Muhammad da yayi mata alkawarin cewa ba zai yi mata kishiya ba a gaban taron daurin aurensu

Kamar yadda ganau ba jiyau ba, Aishat Busari ta bayyana, wata budurwa musulma ta ki karbar sadakinta. Bayan nan sai ta bukaci angon da yayi mata alkwarin cewa ba zai karo kishiya ba a gaban dukkan ‘yan uwansu da suka halarci bikin.

Wannan lamarin ya faru ne a yankin Amuyo da ke Offa a jihar Kwara. Fatima Babawale ta ki karbar sadakinta a yayin daurin aurenta da aka yi a ranar 15 ga watan Fabrairu na 2020 amma ta bukaci babban alkawarin.

A addinin Musulunci, ba dole bane a ba mace sadakinta a matsayin kudi ba. Sadaki na iya zama a wani nau’i na daban da ba kudi ba. Za a iya bada kudi, kayan sanyawa, takalmi ko kuma wani abu daban mai muhimmanci.

A yayin daurin auren Muahhamad Adebayo da Fatima babawale a ranar 15 ga watan Fabrairu, malamin da zai daura auren ya bukaci Muhammad da ya zo ya biya sadakin matar shi. Sannan ya bukaci sanin me zai bata a matsayin sadakin.

KU KARANTA: Gargadi: Yawan shan Paracetamol na iya kashe mutum - Ma'aikaciyar lafiya ta gargadi 'yan Najeriya

A yayin da Muhammad ke dab da aje kudi ne Fatima ta tashi tsaye tare da ce mishi kada ya ajiye. Daya daga cikin malaman ya tambayi me Fatima take so. Sai tace tana bukatar Muhammad yayi mata alkawarin ba zai auro mata ksihiya ba a gaban ’yan uwansu.

Wannan lamari kuwa ya matukar ba Muhammad mamaki don basu taba zantawa a kan hakan da Fatima ba kafin auren.

A take Muhammad ya je wajen iyayen shi inda suka tattauna na mintoci kafin daga bisani suka yanke shawarar yayi abinda amaryar shi ta bukata.

A take ya karba amsa-kuwwa tare da yi mata alkawari. Daga nan aka kammala daurin aure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel