Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka yan bindiga 13 a Zamfara, Kebbi da Katsina

Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka yan bindiga 13 a Zamfara, Kebbi da Katsina

Akalla miyagun yan bindiga 13 ne suka sheka barzahu bayan karanbatta da dakarun rundunar Sojin Najeriya a jahohin Zamfara, Kebbi da Katsina a karkashin aiki na musamman mai taken Operation Hadarin Daji.

Mai magana da yawun Operation Hadari Daji, Kyaftin Abayomi Orii-Orisan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 21 ga watan Feburairu, inda yace aikin ya kaisu ga kwato tarin alburusai da suka kai 4,630 a Moriki dake karamar hukumar Shinkafi na jahar Gusau.

KU KARANTA: Amurka ta haramta ma Najeriya mika $100m daga kudin Abacha ga gwamnan jahar Kebbi

Orisan yace Sojoji sun kashe yan bindiga 8 daga cikinsu har da mace daya, sa’annan sun jikkata wasu da dama a yayin arangama, kuma sun kwato bindiga AK 47 guda 7, babura 22, bindigar toka guda 2, wayoyin salula 4 da jarakuna 30 na man fetir.

Ya cigaba da fadin aikin nasu ya kaisu ga bankado wasu miyagun mutane dake hada kwayoyi marasa kyau, inda suka kwace kwal 350 na ire iren kwayoyin da suke hadawa, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito.

Kauyukan da aikin Sojin ya shafa sun hada da Tungar Mata, Tuduki, Kawaye da Mararraban Kaway dake cikin karamar hukumar Anka na jahar Zamfara, sai kuma Moriki, Belhi, Ruwar Kura, Kyaram, Gallai da Shirkai a karamar hukumar Bukuyum na Zamfara.

Sauran sun hada da Tsauwa, Dankar da Yan Gayya na karamar hukumar Batsari a jahar Katsina, sai kuma kauyukan Gallai, Shirkai da Yarkuka a cikin jahar Kebbi.

Daga karshe Orisan ya isar da sakon babban kwamandan Operation Hadarin Daji, Birgediya Aminu Bande wanda ya tabbatar ma jama’a manufarsu ta cigaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, haka zalika ya nemi yan bindiga su ajiye makamansu domin zaman lafiyansu.

A wani labarin kuma, Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kaduna sun samu nasarar kama wasu miyagun masu garkuwa da mutane guda uku da suka dade suna fitinar jama’an jahar Kaduna, tare ceto wata budurwa daga hannunsu.

Mai magana da yawun Yansandan yankin, Mohammed Jilge ne ya bayyana haka ga menema labaru a ranar Juma’a, 21 ga watan Feburairu a garin Kaduna, inda yace a ranar Laraba suka samu rahoton an sace wata budurwa yar shekara 22 Hadiza Gambo daga Bungel Ladduga na karamar hukumar Kajuru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng