Barkewar sabuwar cuta a Benue: 'Yan majalisa sun bukaci a kebance dan majalisa mai wakiltar yankin

Barkewar sabuwar cuta a Benue: 'Yan majalisa sun bukaci a kebance dan majalisa mai wakiltar yankin

- Wasu ‘yan majalisar wakilai sun bukaci a kebance dan majalisa Samson Okwu a kan cutar da ta barke a yankinsa na jihar Benue

- Dan majalisa James Faleke ne ya fara mika bukatar kebance Okwu din har zuwa lokacin da aka gano musabbabi da kuma wacce irin cuta ce

- Shawarar Faleke ta samu goyon baya ne daga shugaban marasa rinjaye na majalisar, Ndudi Elumelu wanda ya goyi bayan kebance dan majalisar na jihar Benue

Wasu ‘yan majalisar wakilai sun bada shawarar a kebance daya daga cikin ‘yan majalisar da ya fito daga jihar Benue mai suna Samson Okwu, sannan a tantance shi tare da kebance shi sakamakon wata sabuwar cuta da ta barke a yankin Oye-Obi da ke jihar Benue.

‘Yan majalisar sun yi wannan kiran ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrariru a yayin tattaunawa a ka yadda gwamnatin tarayya za ta binciki barkewar cutar a yankin, jaridar The Nation ta ruwaito.

A yayin tattaunawa, James Faleke ne ya mika bukatar yin hakan ga majalisar, har sai zuwa lokacin da aka gano musabbabi da kuma yadda za a magance cutar don gudun yaduwarta.

Wannan shawarar tashi ta samu goyon bayan shugaban marasa rinjaye na majalisar.

Barkewar sabuwar cuta a Benue: 'Yan majalisa sun bukaci a kebance dan majalisa mai wakiltar yankin
Barkewar sabuwar cuta a Benue: 'Yan majalisa sun bukaci a kebance dan majalisa mai wakiltar yankin
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zamfara: Za a koma zaman majalisar jiha a makarantar firamare

Amma kuma, mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Idris Wase, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya ki goyon bayan shawarar. Ya kara da jan kunnen ‘yan uwan aikin nashi da su kiyayi kawo ire-iren wadannan zantukan.

Idan zamu tuna, a yayin da mutuwa ta sanadin cutar Convid-19 ta yawaita, masana kimiyya sun gano maganin da ke warkar da cutar da ta halaka sama da mutane 1500 din.

Kamar yadda wata cibiyar kasar China mai suna Xinhua ta tabbatar, maganin cutar zazzabin cizon sauro mai suna Chloroquine Phosphate na kash ewasu daga cikin alamun cutar mai hatsarin gaske.

A ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairu ne masana kiwon lafiyar suka aminta da cewa za a iya amfani da maganin cikin jerin magungunan da ake ba masu cutar har zuwa warakarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: