Zamfara: Za a koma zaman majalisar jiha a makarantar firamare

Zamfara: Za a koma zaman majalisar jiha a makarantar firamare

Majalisar jihar Zamfara za ta koma wata makarantar firamare inda za ta dinga aiwatar da zaman majalisar da sauran harkokinta. Hakan ya biyo bayan fara gyaran zauren majalisar da za a yi.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamna Bello Matawalle ya bada kwangilar gyaran ginin zauren majalisar. Wannan ya biyo bukatar da Faruku Dosara, shugaban masu rinjaye na majalisar ya mika.

“Ina so in jawo hankalin abokan aikina na bukatar mu koma wani waje daban sakamakon gyaran zauren majalisa da ake yi,” Dosara yace.

Shugaban masu rinjayen ya sanar da sauran ‘yan majalisar cewa zasu koma wata sabuwar makarantar firamare da ke Gusau don ci gaba da aiwatar da zaman majalisa da sauran harkokinsu.

Zamfara: Za a koma zaman majalisar jiha a makarantar firamare
Zamfara: Za a koma zaman majalisar jiha a makarantar firamare
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Bauchi: Dan sanda ya harbi mai babur domin ya hana shi cin hanci ta Naira 50

A yayin bayyana goyon bayan bukatar da Dosara ya bijiro da ita, Hashimu Dansadau ya jawo hankalin ‘yan majalisar a kan amfanin wannan bukata da Dosara ya bijiro da ita.

Kamfanin Dillancin Labarn Najeriya ya ruwaito cewa ‘yan majalisar sun amince da wannan bukata ba tare da wani ja-in-ja ba.

Kakakin majalisar, Nasiru Magarya ya ce majalisar ta amince da hakan ne sakamakon gyaran da ake yi.

“Ba zamu tsayar da aiyukan majalisar ba don haka mun amince da wanan bukatar da Dosara ya bijiro da ita,” yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel