Mutane sun mutu yayin da jiragen sama suka yi taho mu gama a sararin samaniya

Mutane sun mutu yayin da jiragen sama suka yi taho mu gama a sararin samaniya

- Fasinjoji masu tarin yawa sun halaka bayan da jiragen sama biyu suka ci karo a sararin samaniya

- Kamar yadda rahoton ya bayyana, kowanne jirgin daga ciki na dauke da tagwayen inji, matuki da kuma fasinjoji

- Daya daga cikin jiragen saman ya fito ne daga filin tashin jiragen sama da ke kusa da filin amma dayan ba a san daga inda yake ba

Fasinjoji sun halaka bayan jiragen sama biyu sun ci karo a sararin samaniya. Jami'an 'yan sanda sun ce jiragen biyu duk dauke suke da tagwayen injina tare da matukansu hade da fasinjoji. Sun ci karo ne a nisan kafa 4,000 daga kasa a garin Mangalore kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.

Mutane sun mutu yayin da jiragen sama suka yi taho mu gama a sararin samaniya
Mutane sun mutu yayin da jiragen sama suka yi taho mu gama a sararin samaniya
Asali: Facebook

Hotunan wajen hatsarin ya bayyana karafuna a tarwatse a fili da kuma tsakankanin bishiyoyi.

KU KARANTA: Mata 5 sun hadu sun kashe dan uwansu da duka saboda ya nemi a raba gadon mahaifinsu

'Yan sandan sun ce kowanne daga cikin jiragen saman na tafiyarshi ne bisa tsari a sararin samaniyar amma ana ci gaba da bincike.

"Ba mu tabbatar da dalilin da yasa dukkan jiragen saman ke waje daya a lokaci daya ba amma abin alhini ne yadda suka ci karo karo," cewar sifetan 'yan sanda Peter Koger.

Daya daga cikin jiragen saman ya taso ne daga filin tashin jiragen sama da ke da kusanci da wajen, amma dayan ne har yanzu ba a gano daga inda yake ba.

Haka kuma wani matashi a kasar Kenya ya sha dan karen duka wajen 'yan uwanshi mata da yayi sanadiyyar mutuwar shi.

Matan su biyar sun jibgi dan uwan nasu akan ya nemi wani bangare na sadakin daya daga cikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel