Iker Casillas ya yi sallama daga buga wasan kwallon kafa

Iker Casillas ya yi sallama daga buga wasan kwallon kafa

Mun samu labari cewa Iker Casillas ya ajiye wasan kwallon kafa a Duniya bayan ya shafe shekara da shekaru ana gogawa da shi a kungiyoyi irinsu Real Madrid da FC Porto.

‘Dan wasan mai shekaru 38 da haihuwa ya lashe gasar Nahiyar Turai sau uku a Real Madrid. Bayan haka ya taimakawa Real Madrid wajen cin gasar La-liga na Sifen sau biyar.

A shekaru 19 da Iker Casillas ya yi a Real Madrid, ya buga wasanni 725. Casillas yana cikin manyan ‘yan kwallon da aka yi a tarihin kungiyar da kuma kasar Sifen gaba daya.

Casillas ya na ragar Sifen a lokacin da kasar ta samu nasarar cin kofin kwallon kafa na Duniya a shekarar 2010. Wannan shi ne karon farko a tarihi da Sifen din ta taba lashe gasar.

Tsohon Kyaftin din na Real Madrid ya taka rawar gani wajen gasar Euro na Nahiyar Turai da kasar Sifen ta ci a 2008 da 2012. A lokacin shi ne ke rike da kambun Tawagar kasar.

KU KARANTA: Cristiano Ronaldo ya na ba Budurwarsa N32m duk wata

Duk da ficen da Iker Casillas ya yi, Jose Mourinho ya ajiye shi daga babban ‘Dan wasan da ke tsaron ragar Real Madrid a lokacinsa. Kocin ya zabi ya yi aiki da Diego Lopez a 2013.

A shekarar 2016 lokacin da Sifen ta je buga gasar cin kofin Nahiyar Turai a kasar Faransa, aka daina damawa da ‘Dan wasan da ke tsaron raga, aka maye gurbinsa da David De Gea.

‘Dan wasa Iker Casillas ya bar Santiago Bernabeu ne a 2015 bayan rigimarsa da Florentiono Perez. Daga nan ya koma kasar Portugal inda ya bugawa FC Porto na tsawon shekaru hudu.

Casillas ya yi fama da bugun zuciya a bara. Daga nan ya kama hanyar ajiye kwallo. A shekara 38, tsohon ‘Dan wasan ya ce ya yi sallama da wasa, ya kuma fadi inda ya sa gaba yanzu.

Tsohon Golan ya tabbatar da cewa zai yi takarar shugaban kungiyar kwallon kafan kasar Sifen na RFEF. Casillas ya fito shafin Tuwita ya bayyana cewa zai yi takara domin ceto kungiyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng