An kashe sojoji 2 sannan an kona gidaje 150 a Filato
- Yan bindiga a yankin kauyen Gindin Akwati na karamar hukumar Barikin Ladi a jahar Filato sun kashe wasu sojojin Operation Save Heaven biyu
- Har ila yau an zargi sojoji da kona gidaje 150 a matsayin ramuwar gayya
- Kakakin yan sandan jahar Filato, Ubah Gabriel ya tabattar da hari kan sojojin na Gindin Akwati, sannan baya ga sojoji biyun da aka kashe, wani soja ma ya ji rauni
- Ya ce ba a kama kowa ba tukuna amma ana kan gudanar da bincike cikin lamarin
Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga a yankin kauyen Gindin Akwati na karamar hukumar Barikin Ladi a jahar Filato sun kashe wasu sojojin Operation Save Heaven biyu.
Biyo bayan kashe sojojin biyu, an yi zargin cewa jami’an rundunar da ke wanzar da zaman lafiya a Filato da wasu yankunan Bauchi da jahar Kaduna sun kona gidajen Fulani kimanin guda 150 a ranar Talata.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na Najeriya, a karamar hukumar Barkin Ladi, Alhaji Shuaibu Bayero, ya yi zargin cewa jami’an OPSH a motocin Toyota Hilux hudu da babura 11 sun isa kauyukan Dogo, Yelwa, Hayi da mararrabar Gindin Akwati na Barikin Ladi sannan suka cinna wa gidajensu wuta.
Mazauna yankin dai sun bayyana cewa suna cikin damuwa da zullumi sakamakon wannan abu da ya cika da su.
Sai dai an nemi jin ta bakin kakakin rundunar tsaro ta hadin gwiwa da aka dora wa alhakin tabbatar da tsaro a jihar ta Filato, sai dai bai yi wani karin bayani dangane da wannan lamarin ba.
KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: An gano bindigu kirar AK-47 da alburusai a siddin babur (Bidiyo)
Hakazalika kakakin yan sandan jahar Filato, Ubah Gabriel ya tabattar da hari kan sojojin na Gindin Akwati, sannan baya ga sojoji biyun da aka kashe, wani soja ma ya ji rauni. Ya ce ba a kama kowa ba tukuna amma ana kan gudanar da bincike cikin lamarin.
Kan batun kona gidajen, kakakin yan sandan ya ce ba zai iya tabbatarwa ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng