Za a yi bincike kan badakalar kwangilar ginin gidan Gwamnati a Jihar Zamfara

Za a yi bincike kan badakalar kwangilar ginin gidan Gwamnati a Jihar Zamfara

A Ranar Talatar nan, Majalisar dokokin jihar Zamfara ta kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki kwangilar da aka bada na Naira biliyan 2 domin gina sabon gidan gwamnati.

Majalisar ta bakin Honarabul Faruk Musa Dosara ta na zargin cewa gwamnatin Mai girma Abdulaziz Yari Abubakar da ta shude, ta bada aikin gina sabon gidan gwamnati a jihar.

Faruk Musa Dosara ya fadawa Abokan aikinsa a Majalisar dokoki cewa an ware fiye da Niara biliyan biyu da sunan za a gina gidan gwamnati a Zamfara, amma ko fili ba a share ba.

Musa Dosara ya ja hankalin ‘Yan majalisar jihar da cewa takardun da ke gabansa sun nuna masa cewa an zari kudin wannan aiki. ‘Wasu ‘yan majalisa sun goyi bayan ayi cikakken bincike.

Da su ka mike a gaban zauren majalisar, Musa Bawa Musa da Kabiru Magaji Kwatarkwashi sun goyi bayan Musa Dosara, inda su ka ce ya kamata a binciki gaskiyar wannan lamari.

KU KARANTA: Akwai gyara a tafiyar Jam'iyyar APC - Babachir Lawal

Za a yi bincike kan badakalar kwangilar ginin gidan Gwamnati a Jihar Zamfara
Za a gudanar da bincike kan aikin da Gwamnatin Yari ta kashewa kudi
Asali: Twitter

Kakakin majalisa Rt. Hon Nasiru Mu’azu Magarya, ya bada umarni a nada kwamitin mutum bakwai da za su gudanar da dogon bincike, sannan su kawowa majalisar rahoto nan gaba.

Mataimakin kakakin majalisar jihar, Musa Bawa Musa Yankuzo, shi ne shugaban wannan kwamiti. Sauran ‘yan kwamitin sun hada da: Faruk Musa Dosara, da Salihu Usman Zurmi.

Har ila yau, ragowar ‘yan kwamitin su ne: Zaharaddeen M. Sada da kuma Yusuf Alhassan Kanoma. Ana sa ran za su gudanar da cikakken bincike na musamman, su fitar da rahoto.

Wani jigon jam’iyyar APC ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewa gwamnatin Abdulaziz Yari ba ta bada wannan kwangila ba. Ya ce ko da an yi hakan, ‘Dan kwangilan ya kamata a nema.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel