Gwamnonin Jam’iyyar APC sun taya Uwargidar Buhari cika shekara 49

Gwamnonin Jam’iyyar APC sun taya Uwargidar Buhari cika shekara 49

Gwamnonin Jihohin da ke mulki a karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun fito sun taya Matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarta.

A Ranar Talata, 18 ga Watan Fubrairun 2020, gwamnonin na APC a karkashin kungiyarsu, su ka fitar da jawabi domin taya Mai dakin shugaba Buhari murnar cika shekara 49.

Mai girma gwamna Atiku Abubakar Bagudu ne ya fitar da jawabi a madadin gwamnonin APC, ya ce su na taya Uwargidar Najeriya murnar zuwan wannan rana ta musamman.

“Mu a karen kanmu, mu na so mu gode da irin taimakon da ki ke ba kasarmu a matsayin Uwa da kuma kokarin da ki ke yi na musamman wajen nasarorinmu.” Inji Bagudu.

Sanata Atiku Bagudu ya bayyana cewa Uwargidar shugaba Muhammadu Buhari ta na da hangen nesa tare da bada gudumuwa wajen magance kalubalen shugabanci a Najeriya.

KU KARANTA: 2023: Inyamuri ba zai yi mulkin Najeriya ba tukuna- Inji AYCF

Gwamnonin Jam’iyyar APC sun taya Uwargidar Buhari cika shekara 49
Mai girma Aisha Muhammadu Buhari ta cika shekaru 49
Asali: Twitter

“Mu na taya ki murnar a wannan rana ta musamman da ke da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari.” Bagudu ya kira Buhari da fitilar gwamnatin APC.

“A matsayinki na Uwargidar Najeriya, kin kawo dabaru da su ka taimaka wajen ganin mun cika alkawarin da mu ka yi wa ‘Yan Najeriya na kawo masu canji a mulki.”

Bayan haka, Atiku Bagudu, a madadin sauran gwamnonin sun taya Takwaransu, Nasir El-Rufai murnar cika shekar 60 a Duniya. Bagudu ya yabawa kokarin gwamnan.

“A matsayin gwamnan jihar Kaduna, ta hanyar manufofin da gwamnatin ka ta APC ta kawo, ka na wakiltar fitilar siyasarmu ta jam’iyyar APC.” Inji kungiyar gwamnonin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng