Murnar zagayowar ranar haihuwa: El-Rufa'i ya dauki hotuna tare da dukkan matansa (Hotuna)

Murnar zagayowar ranar haihuwa: El-Rufa'i ya dauki hotuna tare da dukkan matansa (Hotuna)

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya dauki hoto a cikin jama'a tare da dukkan matansa yayin murnar cikarsa shekaru 60 a duniya.

Gwamnan, tsohon minstan birnin tarayya, Abuja, yana auren mata uku, kuma dukkansu sun halarci taron liyafar taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Fadar shugaban kasa ta aika sakon taya murna tare da yin ruwan kalamai masu dadi ga El-rufa'i a cikin wani jawabi da ta fitar.

"A yayin da gwamna El-Rufa'i ya cika shekara 60, fadar shugaban kasa ta yi imanin cewa basirarsa da kwazonsa da hikima zasu cigaba da habaka tare da ware shi daban a cikin sauran shugabanni.

Murnar zagayowar ranar haihuwa: El-Rufa'i ya dauki hotuna tare da dukkan matansa (Hotuna)
El-Rufa'i matansa uku
Asali: Twitter

"Buhari da shugaban kasa sun san cewa El-rufa'i ya shiga aikin gwamnati ne bisa kaddara, amma kuma gudunmawar da ya ke bayar wa a bangaren mulki da shugabanci suna da matukar muhimmanci da tasiri. Yana daga cikin fitattun 'yan Najeriya da suka taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samu canjin gwamnati a shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Dangin amarya sun lakada wa ango duka a wurin liyafar biki (Hotuna)

"Fadar shugaban kasa tana mai addu'ar Allah ya cigaba da yi wa jihar Kaduna da iyalin El-Rufa'ai albarka, da bashi koshin lafiyar cigaba da aiyukan alherin da yake yi," a cewar jawabin da fadar shugaban kasa ta fitar domin taya El-Rufa'i murnar cikar shekara 60.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel