An tsaurara matakan tsaro yayinda yan APC ke zanga-zangar a tsige Oshiomhole

An tsaurara matakan tsaro yayinda yan APC ke zanga-zangar a tsige Oshiomhole

An tsaurara matakan tsaro a mashigin sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a Abuja yayinda mambobin jam’iyyar ke zanga-zangar a tsige shugabansu na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole.

An kawo wata motar Hilux na yan sanda an girke a sakatariyar jam’iyyar ta kasa domin taimaka wa jami’an tsaro wajen wanzar da zaman lafiya a zanga-zangar.

Har ila yau n ajiye motar Hilux kirar Nissan na hukumar DSS pake a kusa da mashigin sakatariyar.

An tsaurara matakan tsaro yayinda yan APC ke zanga-zangar a tsige Oshiomhole
An tsaurara matakan tsaro yayinda yan APC ke zanga-zangar a tsige Oshiomhole
Asali: UGC

Zanga-zangar na “dole Oshiomhole ya tafi” ya kasance na biyu a cikin mako guda kamar yadda masu zanga-zangar suka yi a ranar Litinin, inda suka bukaci a tsige Shugaban APC na kasa.

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce Za su ci gaba da zanga-zangar har sai an tsige Oshiomhole.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da Kyaftin Nuhu a matsayin Shugaban NCAA

“A matsayinmu na jam’iyyar mun yi rashi asara daban-daban sakamakon kasancewar Oshiomhole a matsayin shugaba,” in ji shi.

A wani labarin kuma mun ji cewa tsohon Sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir David Lawal, ya yi wata doguwar hira da Premium Times inda ya tattauna game da batun gwamnati, siyasar APC da shugabancin kasa.

Babachir David Lawal ya nuna cewa ya na ganin darajar Bisi Akande a matsayinsa na Dattijo, amma ya nuna shakkun samun nasara game da aikin da kwamitinsa zai yi na sulhu a APC.

Ganin yadda APC ta rasa Ribas, Zamfara, da wasu Jihohi, Lawan ya nuna cewa dole sai Adams Oshiomhole da mutanesa sun kara kokari wajen ganin jam’iyyar ba ta fadi zabe a 2023 ba.

Tsohon SGF din ya kuma yi magana game da kwaskwarimar da Majalisa za ta yi wa tsarin mulki. A na sa shawarar, zai yi kyau Najeriya ta koma amfani da Majalisa guda domin rage kashe kudi.

A kan rikicin Boko Haram, Lawal ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne ace abubuwa su na tabarbarewa. Lawal ya ce an samu cigaba, kuma shugaban kasa ya san yadda za a kawo gyara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng