Tashin hankali: Yan bindiga sun kashe sojoji 4 da yan farar hula 2 a Bayelsa
- Yan bindiga sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke dauke da mai a hanyar kogin Lutegbene, yankin karamar hukumar Ekeremor da ke jahar Bayelsa
- Sun kashe sojoji hudu da ke yiwa jirgin ruwan rakiya da kuma wasu yan farar hula guda biyu
- Hakan ya haddasa rashin kwanciyar hankali a yankin yayinda aka zuba dakarun sojoji yankin, inda suka bukaci mazauna yankin su fito da masu laifin
- An tattaro cewa fusatattun sojoji sun fara kone-konen wasu gidaje a yankin sakamakon rashin fito da masu laifin da mazauna yankin basu yi ba
Wasu yan bindiga sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke dauke da mai a hanyar kogin Lutegbene, yankin karamar hukumar Ekeremor da ke jahar Bayelsa.
An tattaro cewa sun kashe sojoji hudu da ke yiwa jirgin ruwan rakiya da kuma wasu yan farar hula guda biyu.
An rahoto cewa sauran wadanda ke cikin jirgin sun tsere cikin kogin da raunuka sakamakon harbin bindiga.
Lamarin, wanda ya afku a daren ranar Asabar, ya haddasa rashin kwanciyar hankali a yankin yayinda aka zuba dakarun sojoji yankin, inda suka bukaci mazauna yankin su fito da masu laifin.
Majiyoyi wadanda suka tabbatar da ci gaban, sun ce fusatattun sojoji sun fara kone-konen wasu gidaje a yankin sakamakon rashin fito da masu laifin da mazauna yankin basu yi ba, jaridar The Nation ta ruwaito.
Wata majiya daga yankin, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce sojojin na yiwa jirgin ruwan rakiya ne daga Port Harcourt a jahar Rivers zuwa Warri a jahar Delta lokacin da aka far masu da harin.
Sai dai ba a tabbatar da zargin cewa sojoji na kone-konen gidaje ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya gabatar wa da alkalan babbar kotu manyan motocin alfarma guda 24
An tattaro cewa kakakin rundunar sa-kai, na Operation Delta Safe, Eromosele Unuakhalu, bai amsa kiran wayarsa ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng