El-Rufai ya gabatar wa da alkalan babbar kotu manyan motocin alfarma guda 24

El-Rufai ya gabatar wa da alkalan babbar kotu manyan motocin alfarma guda 24

Gwamna Nasir El-Rufai na jahar Kaduna ya gabatar da manyan motoci kirar Jeep guda 24 ga alkalan babbar kotu, duk daga cikin kokarinsa na inganta jin dadin jami’an bangaren shari’a a jahar.

Gwamnan, a yayin gabatar wa da alalai motocin a Kaduna ya bayyana cewa za a samar da Karin motoci ga sauran alkalai.

El-Rufai ya kuma bayyana tsare-tsaren gwamnati na gina wa alkalan gidaje.

El-Rufai ya gabatar wa da alkalan babbar kotu manyan motocin alfarma guda 24
El-Rufai ya gabatar wa da alkalan babbar kotu manyan motocin alfarma guda 24
Asali: UGC

“Wadanda za su amfana na gaba sune Khadis na kotun daukaka kara na shari’a da alkalan kotun daukaka kara na al’ada, In shaa Allah kwanan nan za a gabatar masu da su, ba wai alkalai masu shigowa kadai ba a’a harma da wadanda suke nan tun da can.

“Gwamnatin jahar na shirin samar da gidaje ga manyan akalai, domin a yanzu alkalai na zaune ne a ginin gwamnati daban-daban a fadin jahar.

“Mun yarda cewa idan har muka samar da gidaje inda dukkanin manyan lauyoyi za su kasance cikin wadata, da wajen shaktawa da wajen siye-siye, za su kasance da wadatar zuci da ingantaccen tsaro.

“Muna aiki k haka kuma kwanan nan masu aiki za su tunkari shugabannin kotuna don duba tsarin da zai fi dacewa,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Jamian tsaro sun mamaye kotun koli yayinda ake shirin sake duba shariar Imo da Zamfara

Gwamnan ya kara da cewa gwamnati na aiki kan tsarin gine-gine na bayan ritaya ga ma’aikatan shari’a, domin yana daya daga cikin lamuran da suka addabi mafi akasarin ma’aikatan gwamnati yayinda suke tunkarar yin ritaya.

Ya kara da cewa, gwamnati na shirin samar da cibiya guda ga dukkanin kotuna Kaduna maimakon yadda suke a tarwatse a wurare daban-daban.

A wani labarin kuma, mun ji cewa majalisar wakilai ta yi odan motocin alfarma guda 400 kirar Toyota Camry 2020 domin amfanin yan majalisar su 360, kamar yadda shuwagabannin majalisar suka yanke hukunci a wani taro da suka yi a ranar 5 ga watan Feburairu.

Jaridar Punch ta ruwaito wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da amincewar majalisar na sayo motocin alarma guda 400, sai bata bayyana farashin da majalisar za ta sayo motocin a kai ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel