Ma’aikatan Hukumar JAMB sun fada hannun Miyagu a titin Abuja-Lokoja

Ma’aikatan Hukumar JAMB sun fada hannun Miyagu a titin Abuja-Lokoja

Wasu ma’aikata hudu na hukumar jarrabawa ta JAMB, sun shiga hannun masu garkuwa da mutane yayin da su ke tafiya a babban titin Abuja zuwa Lokoja.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa wadannan ma’aikatan sun fito ne daga Hedikwatar hukumar ta JAMB inda su ka kama hanyar zuwa Garin Kabba a jihar Kogi.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace su ne a daidai yankin Lokoja/Obajana/Kabba a jihar Kogi. Wannan abu ya faru ne a Ranar Lahadi, 16 ga Watan Fubrairu, 2020.

Ma’aikatan na JAMB sun bar Abuja, sun kama hanyar Garin Kabba ne da nufin shirya wata jarrabawa ta masu shirin shiga makarantun gaba da sakandare.

Wadanda abin ya auku a idonsu sun bayyanawa cewa ‘Yan bindigan sun tare hanya ne, sannan su ka kama ma’aikatan, su ka shiga da su cikin kungurmin daji.

KU KARANTA: An sace wani babban jami'in gwamnati a Jihar Nasarawa

Ma’aikata Hukumar JAMB sun fada hannun Miyagu a titin Abuja-Lokoja
An dade ana dauke mutane a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja
Asali: Facebook

Rundunar ‘Yan Sanda ta bakin Kakakinta na jihar Kogi, DSP William Ayah, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, amma ya ce su na kokarin ceto ma’aikatan.

DSP William Ayah ya fadawa Manema labarai cewa sun tura Dakaru na musamman na F-SARS, su shiga cikin dajin domin ceto wadannan Bayin Allah da aka dauke.

William Ayah ya kuma bayyana cewa an yi dacen ceto wani daga cikin ma’aikatan hukumar da aka sace. Wani mai suna Hamzah, daga cikinsu ya kubuta a yanzu.

Yanzu haka Hamzah ya na asibiti inda ake duba lafiyarsa inji Rundunar ‘Yan Sandar. Hukumar JAMB, ta tabbatar da cewa ta na yunkurin ganin ta ceto Jami’an na ta.

Mista Fabia Benjamin wanda ke magana a madadin hukumar jarrabawar, ya ce an hada-kai da Jami’an tsaro domin a fito da wadannan ma’aikata da aka yi garkuwa da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel