Duniya ta na taya Aisha Buhari murnar cika shekaru 49 da haihuwa

Duniya ta na taya Aisha Buhari murnar cika shekaru 49 da haihuwa

A yau 17 ga Watan Fubrairun 2020 ne ake taya Mai dakin Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari watau Hajiya Aisha Muhammadu Buhari zagayowar ranar haihuwarta.

Mun kawo takaitaccen tarihin Uwargidar Najeriyar wanda ta cika shekaru 49 yau a Duniya.

1. Haihuwa

An haifi Aisha Muhammadu Buhari ne a shekarar 1971 a Jihar Adamawa. Mahaifin ta Injiniyan manyan hanyoyi ne yayin Mahaifiyar ta Diyar Manoma ce. Kakanta, Mohammed Ribadu, shi ne Ministan tsaro na farko a Najeriya.

2. Aure

Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta yi aure da tsohon shugaban kasa a lokacin watau Muhammadu Buhari. An yi wannan aure ne a shekarar 1989. A wancan lokaci Hajiya Aisha Buhari ta na da shekara 18 ne a Duniya.

KU KARANTA: Iyalin Shugaban kasa Buhari da Mai dakinsa Aisha Buhari

Duniya ta na taya Aisha Buhari murnar cika shekaru 49 da haihuwa
Aisha Muhammadu Buhari ta auri Shugaban Najeriya ne shekaru 30 da su ka wuce
Asali: Depositphotos

3. Karatu

Uwargidar shugaban Najeriyar ta fara karatunta na Firamare da Sakandare a Adamawa. Bayan ta yi aure, ta yi Digiri a Jami’ar Amborse Ali, ta kuma yi Digirgir a NDA. Aisha ta samu shaidar Difloma ta PGD a harkar kwalliya a Faransa.

4. Aikace-aikace

A da can Aisha Buhari ta na da shagon gyaran gashi. Ta kuma rubuta littatafai kan yadda ake kwalliya. A matsayin Uwargidar shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta kafa kungiya ta Future Assured wanda ta ke taimakawa Marasa galihu.

5. ‘Ya ‘ya

A sakamakom aurenta da Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari ta samu ‘Ya ‘ya biyar. Wadannan ‘Ya ‘ya su ne: Halima Buhari-Sheriff, Yusuf Muhammadu Buhari, Zahra Buhari-Indimi, Hannan Buhari da kuma 'Yar auta Amina Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel