Yanzu Yanzu: Kotu ta yi umurnin kama tsohon Shugaban Kwastam, Dikko
Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da izinin kama tsohon Shugaban kwastam din Najeriya, Abdullahi Inde Dikko kan ci gaba da kin halartan zaman kotu domin amsa wani tuhumar damfara da hukumar yaki da rashawa ta ICPC ke yi a kansa da wasu mutum biyu.
Justis Ijeoma Ojukwu, yayinda ta ke umurnin kama Dikko a ranar Alhamis, ta bayyana cewa lauyansa, Solomon Akuma (SAN) wanda a zaman karshe, ya bayar da tabbacin cewa wanda ya ke karewa zai hallara gaban kotu a yau, ya zo da wani takardar asibiti, inda ya yi ikirarin cewa Dikko na cikin tsananin rashin lafiya kuma an kwantar dashi a asibitin Landan.
Justis Ojukwu ta bayyana cewa adireshin Dikko, kamar yadda ya ke kunshe a rahoton asibitin - No: N6 Amhed Musa Crescent Jabi, Abuja – bai yi daidai da ikirarin lauyansa na cewa Dikko na kwance a asibitin Landan ba.
Don haka mai shari’ar ta bayyana cewa idan yan sanda suka gano cewa da gaske Dikko na kwance a wani asibitin Landan, ton za a dage umurnin.
Ta kara da cewa idan kuma aka samu akasakin haka, toh yan sanda su kama Dikko sannan su gurfanar dashi a gaban kotu a ranar 16 ga watan Maris, 2020, wanda ya kasance ranar zama na gaba.
A tuhumar mai lamba: “FHC/ABJ/CR/21/2019, an ambaci sunan Dikko da wasu mutane biyu – wani tsohon mataimakin Shugaban kwastam da ke kula da fannin kudi, Garba Makarfi da Umar Hussaini, wani lauya a matsayin wadanda ake kara.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Babu wanda ya kai mani hari a jahar Kaduna – Ministan sufuri
Dikko, Makarfi da Hussaini na cikin wadanda ake zargi da sanya Manajan Darakta na kamfanin Cambial Limited, Yemi Obadeyi, biyan naira biliyan 1.1 a asusun ofishin Capital Law a matsayin kudin siyan wajen kwanan jami’an hukumar kwastam na Najeriya da aka dawo dashi.
An tattaro cewa Hussaini ya rarraba kudin zuwa asusun bankuna daban-daban, inda shi ya tashi da dala miliyan uku.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng