Bayelsa: Sabon zabe ya kamata a shirya gaba daya – Oshiomhole ga hukumar INEC
Mun fahimci cewa jam’iyyar APC ta na neman hukumar zabe na kasa mai zaman kanta watau INEC ta sake shirya wani zabe dabam domin fitar da gwamnan jihar Bayelsa.
APC wanda ta rasa kujerar Bayelsa a kotun koli, ta fito ta na cewa Douye Diri bai cancanta ya zama gwamna ba, domin bai cika sharudan da doka ta gindaya na lashe zabe ba.
A wata wasika da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya aikawa hukumar zabe, ya bayyana cewa ya sun yi na’am da hukuncin da kotun koli ta yi a makon jiya.
Amma duk da hakan, Adams Oshiomhole, ya hakikance a kan cewa Douye Diri na PDP da INEC ta ba shaidar lashe zabe kamar yadda aka bukata, bai cancanci zama Gwamna ba.
Kamar yadda mu ka samu labari daga Premium Times, Adams Oshiomhole ya rubuta wannan takarda ne ya na kalubalantar mulkin da aka ba PDP da ta zo na biyu a zaben bara.
KU KARANTA: Mulkin Jihar Bayelsa zai dawo hannun APC - Tsohon Gwamna
Kwamred Oshiomhole, a madadin jam’iyyar APC, ya fadawa INEC cewa Douye Diri ya samu 2/3 na kuri’un da aka kada a zaben ne a cikin kananan hukumomi biyar a maimakon shida.
A dokar zabe dole ‘Dan takara ya samu nasara a cikin kashi 2/3 na kananan hukumomi (a zaben jiha) ko kuma 2/3 na jihohi (a babban zaben shugaban kasa) kafin ya iya lashe zabe.
Shugaban Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ya kamata ace PDP ta samu wadannan kuri’u ne a cikin kananan hukumomi shida ake da su a cikin jihar Bayelsa kafin a iya ba ta mulki.
Hukumar INEC ta nuna cewa Douye Diri ya cika duk wasu sharudan zama gwamna, don haka ta mika masa shaida lashe zabe kamar yadda Alkalan kotun koli su ka bada umarni.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng