Bayelsa: Za a dawowa Jam’iyyar APC da nasararta - Inji Timipre Sylva

Bayelsa: Za a dawowa Jam’iyyar APC da nasararta - Inji Timipre Sylva

A jihar Bayelsa ana ganin yadda siyasa da kotu su ke aiki, inda jam’iyyar PDP ta shige gidan gwamnati a lokacin da ake sa ran jam’iyyar APC za ta karbe mulki.

Timipre Sylva wanda shi ne karamin Ministan man fetur a Najeriya, ya fito ya na bayyana cewa mulkin jihar Bayelsa zai koma hannun jam’iyyar APC nan gaba kadan.

Duk da kotun koli ta ruguza nasarar David Lyon da APC, Cif Timipre Sylva ya ce za a dawowa jam’iyyar APC nasarar da ta samu a zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Jaridar The Nation ta rahoto Ministan ya na cewa Lauyoyin APC za su bi duk wata kafa da ta rage a shari’a domin ganin mulki ya koma hannun jam’iyyar APC a Jihar.

Mai girma Ministan ya yi wannan jawabi ne a Ranar Lahadi, 16 ga Watan Fubrairun 2020, kamar yadda mu ka samu labari, ya na mai jan hankalin duk Masoyansu.

KU KARANTA: Ana lallabar jigon PDP ya janye karar da ya shigar a kan Gwamnan Bayelsa

Bayelsa: Za a dawowa Jam’iyyar APC da nasararta - Inji Timipre Sylva
Timipre Sylva ya ce Lauyoyin APC za su yi kokarin karbe Bayelsa
Asali: UGC

Cif Timipre Sylva ya roki Mutanen jihar Bayelsa da cewa su guji yin abin da zai jefa jihar cikin wata matsala, tare da kiransu da cewa ka da su dauki doka a hannunsu.

A jawabin na sa, tsohon gwamnan ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari hakuri na jagwalgwala masa lissafi bayan an shirya zuwansa Bayelsa a makon jiya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi niyyar zuwa Garin Yenagoa domin ya halarci bikin rantsar da David Lyon. A karshe dole shugaban kasar ya hakura da wannan tafiya.

APC ta na ikirarin cewa PDP da ‘Dan takararta, Douye Diri, ba su samu akalla 25% na kuri’un da aka kada a biyu cikin ukun kananan hukumomin da ke jihar Bayelsa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel