Boko Haram sun ki karbar kudi domin su saki Leah Sharibu – Majiyar Gwamnati

Boko Haram sun ki karbar kudi domin su saki Leah Sharibu – Majiyar Gwamnati

‘Yan kungiyar Boko Haram sun yi watsi da kudin fansar da gwamnatin tarayya ta nemi ta ba su domin su saki Leah Sharibu da ta ke tsare a hannun su na tsawon wata da watanni.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa Jaridar Daily Trust jiya cewa gwamnati ta yi niyyar ba ‘Yan ta’addan miliyoyin da su ka bukata da nufin wannan yarinya ta kubuta.

Leah Sharibu ta na cikin ‘Yan makarantar mata fiye da 100 da aka sace a Garin Dapchi, ‘Yan ta’addan sun saki wadannan yara illa Sharibu wanda har yanzu ta ke tsare a hannunsu.

A cewar Majiyar, gwamnati ta shirya tsaf domin ba Boko Haram miliyoyin kudin da su ka bukata, sai da aka shirya za a mika masu wannan kudi, sai Boko Haram su ka canza shawara.

Gwamnatin tarayya ta cin ma yarjejeniya tsakanin kafar da za a mika kudin da jami’an tsaron gwamnati, an shafe fiye da wata guda ana ta faman je-ka-ka-dawo, inji Majiyar gwamnatin.

KU KARANTA: Ba mu kashe 'Yan ta'adda 250 ba - Sojojin saman Najeriya

Boko Haram sun ki karbar kudi domin su saki Leah Sharibu – Majiyar Gwamnati
Gwamnati ta nemi Boko Haram su karbi kudi su saki Leah Sharibu
Asali: UGC

Wani daga cikin wanda ya san yadda lamarin ya ke, ya bayyana cewa gwamnati ta na kokarin ganin ta ceto Leah Sharibu da duk wadanda su ke tsare a hannun ‘Yam kungiyar Boko Haram.

A cewarsa, ‘Yan ta’addan su na neman su yi amfani da addinin wannan Yarinya ne domin su raba kan Musulmai da Kiristoci, wanda hakan ya na iya kawo mummunan sabani a cikin kasar.

Kokarin raba kan jama’a da kawo tashin-tashina ne ya sa ‘Yan ta’addan su ka ki karbar kudin da su ka yi da gwamnati, su ka zabi su cigaba da tsare wannan yarinya da aka dauke tun 2018.

Fadar shugaban kasa za ta cigaba da kokarin wajen ganin an ci ma nasarar kubuto da wannan Baiwar Allah. Idan ba haka ba za a zargi gwamnatin Buhari da gazawa wajen kare ran ta.

Mahaifinta, Nathan Sharibu ya shaidawa Jaridar cewa bai da labarin cewa ‘Yan Boko Haram sun ki karbar fansar da su ka sa wa gwamnati. Iyayen yarinyar su na addu’ar sake ganin Diyarsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel