Zaben neman aure a Giade shirme ne – Mahaifin yaron da ya ci zabe

Zaben neman aure a Giade shirme ne – Mahaifin yaron da ya ci zabe

Rahotanni sun kawo cewa Iyayen saurayin da ya yi nasara a zaben da aka gudanar tsakanin 'yan takarar neman auren wata budurwa mai suna Hajara a garin Giade da ke jahar Bauchi, sun yi watsi da abin a matsayin "shirme da shiririta".

Labarin yadda mutane suka jefa kuri'ar raba gardamar a a garin Giade na jihar Bauchi ya karade kafafen intanet a makon nan.

Kafafen sun ruwaito yadda wata budurwa ta bukaci mutanen gari su yi alkalanci tsakanin samarinta biyu da ta ce tana son su kuma tana gudun a zarge ta da yaudara.

Sai dai a hira da shafin BBC ta yi da Malam Danladi Ibrahim, kawun saurayin da ya yi nasara a zaben, ya bayyana cewar wasa ne tsakanin yara amma aka yi ta yadawa a shafukan zumunta.

A cewar Danladin shi dakansa jin labarin ya yi a wajen wadansu mutane, sannan ya nemi ba'asi sai aka yi masa bayani cewa maganar yara ce.

Zaben neman aure a Giade shirme ne – Mahaifin yaron da ya ci zabe
Zaben neman aure a Giade shirme ne – Mahaifin yaron da ya ci zabe
Asali: Twitter

Ya ce: "To da aka fada mani haka sai aka ce ai irin wasan nan ne na yara, shi ne har aka dora shi a kan Facebook da Whatsapp."

A cewarsa yaron bai wuci shekara 16 da haihuwa ba, bai isa aure ba sannan ba shi da masaniyar cewa yaron na da wata budurwa.

"To wannan dai shi ne gaskiyar maganar abin da na fada maka: shiririta ce da ma irin ta yara, suka je suka yi ta.

"Ni kaina wallahi da aka kira ni jiya aka fada mani kusan kwana na yi ban yi barci ba, ban rintsa ba, abin ya dame ni," in ji shi.

Ya ce shi bai taba sanin cewa yaron na da budurwa ba kuma budurwar da ake magana a kanta ba ita ce aka sanya hotonta tare da yaron ba, a cewarsa ta hoton yarsa ce kuma ita ce yayar yaron da ake magana a kai.

A baya dai mun ji cewa n gudanar da wata 'yar kwarya-kwaryar zabe a jihar Bauchi domin a raba gardama tsakanin wasu samari biyu da ke neman auren wata budurwa guda bayan budurwar ta kamu da son samarin biyu da kuma gaza zaban daya daga cikinsu.

A cewar wani mai amfani da shafin Twitter @Mubarack_Umar, budurwar mai suna Khadija ta kamu da son mazan biyu, Inusa da Ibrahim a garin Giade da ke jihar Bauchi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya bayyana matsayarsa a kan harin Katsina

Bayan da gaza tsayar da guda cikinsu da za ta aura, manyan gari suka yanke shawarar yin zabe domin wanda ya lashe zaben ya zama angon budurwar.

Mutane sun fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'unsu inda daga karshe Inusa ne ya yi nasara da kuri'u mafi rinjaye kuma an mika masa takardan shaidan cin nasarar zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel