Ban da wata niyyar sake aure a yanzu – Inji Janar Babangida

Ban da wata niyyar sake aure a yanzu – Inji Janar Babangida

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi hira da gidan Jaridar Daily Trust, har ya tattauna game da abubuwan da su ka shafi rayuwarsa.

Maryam Babangida wanda ta kasance Uwargidar Najeriya na shekaru takwas tsakanin Agustan 1984 zuwa 1993 ta rasu ta bar Maigidanta bayan sun shafe shekaru 40 tare.

Da aka tambayi Janar Babangida game da yadda ya ke rayuwar gwauranta a matsayinsa na ‘Dan shekara 78 a Duniya, sai ya bayyana cewa ‘Ya ‘yansa su na taimaka masa.

Kwanakin baya an yi ta yadawa cewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya na neman Matar aure, amma wannan karo, ya ke cewa wannan aikin ‘Yan jarida ne kurum.

“Abin da ‘Yan jarida su ke so kenan. Mutane su na ta tambayata, na kuma fada masu cewa wannan abin da ku (‘yan jarida) ku ka fada ne, bai nufin abin da na fada kenan.”

KU KARANTA: Babangida ya fadi yadda za a kawo karshen yakin Boko Haram

Ban da wata niyyar sake aure a yanzu – Inji Janar Babangida
Babangida ya na kallo Maryam Babangida ta mutu a gadon asibitin Amurka
Asali: Facebook

“Ina da ‘Ya ‘ya masu fahimta da kula sosai; su na kokarin dasawa daga inda Mahaifiyarsu ta bari.”

Tsohon shugaban na Najeriya ya ce ‘Ya ‘yan cikinsa sun tisa daga inda Mahaifiyarsu ta bari. Maryam Babangida ta rasu ne a sakamakon fama da cutar daji watau kansa.

IBB ya tabbatar da cewa a wannan shekaru na sa, bai tunanin sake aure. A halin yanzu, tsohon Sojan ya ce babu abin da ya ke yi a yanzu sai dai hutu da barci da karatu.

Haka zalika da aka yi masa tambaya game da karatun Al-Kur’ani, Babangida, ya nuna cewa zai fi kyau ace jama’a ba su san labarin yadda ya ke yawan karatun Al-Kur’ani ba.

Ibrahim Babangida ya auri Maryam ne daf da za a fara yakin basasa a shekarar 1969. Ainihin Maryam Mutumiyar kasar Delta ce a yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel