Yanzun nan: An yi garkuwa da babban jami'in gwamnatin Nasarawa
- Yan bindiga sun yi garkuwa da sakataren din-din-din na ma’aikatar ayyukan a jahar Nasarawa, Alhaji Jibrin Giza
- Lamarin ya afku ne a tsakar daren ranar Asabar
- Kwamishinan yan sanda a jahar, Mista Bola Longe, ya tabbatar da lamarin ga manema a Lafia
Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da sakataren din-din-din na ma’aikatar ayyukan a jahar Nasarawa, Alhaji Jibrin Giza, a tsakar daren ranar Asabar.
Kwamishinan yan sanda a jahar, Mista Bola Longe, ya tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a Lafia.
Longe ya fada ma NAN cewa yan bindiga sun sace sakataren din-din-din din daga gidansa a Shabu, wani yanki na Lafia da misalin 12:40 na tsakar dare zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Asali: Twitter
A cewar kwamishinan yan sandan, Shugaban yan sanda a yankin ya rigada ya zuba wasu jami’ai wadanda za su bi sahun masu garkuwan da suka tsere da wadanda suka sace.
Longe ya kara da cewa ya umurci mataimakin kwamishina na ayyuka, jami’in da ke kula da rundunar yaki da fashi na musamman, da su kakkabe yankin don tabbatar da sun ceto wadanda aka sace da kuma kama masu garkuwan.
Ya kuma sha alwashin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta ceto wadanda aka sace.
Longe ya kara da cewa masu garkuwan ba su kira yan’uwan wadanda suka sace ba tukuna.
A wani labarin kuma mun ji cewa Wani sabon ango mai suna Chidubem ya saki matarsa mai suna Vivian Chidinma bayan wani tsokaci da tayi a kan yadda mata zasu kashe mazansu masu cin amana a saukake.
A wani tsokaci da Chidubem ya ga matarsa tayi a wani dandali a kafar sadarwa ta Facebook mai suna “Extraordinary mums and singles”, hankalin sabon angon ya matukar tashi.
Matar ta nuna goyon bayanta ga mata masu kashe mazansu da ke cin amanarsu.
KU KARANTA KUMA: Shekau ya yi barazanar kai ma gidan rediyon BBC, Bukarti da Minista Pantami hari
Ta shawarci matan su dau dabararta a maimakon saka wuka su kashe miji wanda hakan ke jefa su cikin babbar matsala.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng